Tattalin Arzikin Ghana Ya Bunkasa Da Kashi 5.7 A Shekarar 2024
Published: 16th, March 2025 GMT
Hukumar kididdiga ta kasar Ghana ta ce, tattalin arzikin Ghana ya bunkasa da kashi 5.7 cikin 100 a shekarar 2024, sakamakon gagarumin aikin masana’antu, a daidai lokacin da ake gudanar da sauye-sauyen tattalin arzikin kasar da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ke marawa baya.
Da yake jawabi ga manema labarai jiya litinin a Accra, babban birnin Ghana, Babban jami’in kididdiga na gwamnatin kasar, Samuel Kobina Annim, ya ce bunkasar tattalin arzikin ya kai kashi 2.
Ya kara da cewa, “Duk da an samu tafiyar hawainiya a karuwar kashi 0.2 cikin 100 a rubu’i na hudu, bangaren masana’antu ya jagoranci ci gaban tattalin arzikin Ghana a shekarar 2024 tare da samun karuwar kashi 7.1 cikin 100, sakamakon ayyukan gine-gine da ma’adinai da fasa duwatsu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tattalin arzikin
এছাড়াও পড়ুন:
Netanytahu Ya Fusta Da Furucin Kasar Canada Akan Kisan Kiyashi A Gaza
Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.
Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai.
Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa, bai ji kamlar kisan kiyashi ba, a cikin abinda aka ambata.
Wannan bai hana Fira ministan na HKI sukar takwaransa na Canada ba,tare da bayyana shi a matsayin mai kin jinin yuhudawa.
Su kuwa kungiyoyin kare hakkin bil’adama na cikin kasar Canada sun bayyana ja da bayan da Fira minstan ya yi da cewa, ba abinda za a laminta da shi ba ne, ya zama wajibi a gare shi da ya goyi bayan MDD da kungiyoyin kasa da kasa na kare hakkin bil’adama akan cewa; Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.
Alaka a tsakanin HKI da kuma kasar Canada suna kara kamari,a lokacin da kungiyoyin kasa da kasa suke kara yi wa Tel Aviv matsin lamba akan kawo karshen yakin da take yi a Gaza.