Aminiya:
2025-03-17@00:15:55 GMT

El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi

Published: 17th, March 2025 GMT

Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta buƙaci Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwar ɗaliban malamin bisa abin da ta kira rashin adalci da aka musu.

Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za su maka shi a kotu.

An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma

Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da gidauniyar ta fitar, wadda Sayyadi Aliyu Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya sanya wa hannu.

A cewar takardar, dole ne El-Rufai ya fito ya yarda da laifinsa sannan ya nemi afuwar gidauniyar, ɗalibanta da jagoranta, Sheikh Ɗahiru Bauchi.

Gidauniyar ta zargi tsohon gwamnan da bayar da umarni ga jami’an tsaro don su kai samame a makarantun tsangayar Sheikh Ɗahiru Bauchi, inda aka kama wasu ɗaliban karatun Alƙur’ani har zuwa gidansa.

Har yanzu, akwai ɗaliban da ba a san inda suke ba.

Sayyadi ya bayyana cewa an yi hakan ne da gangan domin a tozarta Sheikh Ɗahiru Bauchi da kuma hana ci gaban ilimin addini da ya ke yi.

Ya ce idan har El-Rufai bai nemi afuwa ba kafin ƙarshen Ramadan, za su kai ƙararsa ga Shugaban Ƙasa, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, da kotu.

Idan kuwa duka ba su yi musu adalci ba, za su mika ƙarar ga Allah ta hanyar addu’a.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gidauniya Neman Afuwa Sheikh Ɗahiru Bauchi Sheikh Ɗahiru Bauchi

এছাড়াও পড়ুন:

An kama malama tana lalata da ɗalibinta

An kama wata malamar makarantar sakandare ta California a Amurka da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17.

Wannan da ba shi ne karon farko ba da aka tuhumi wani da irin wannan hali ba a makaranatar.

Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa

An kama malama Dulce Flores, mai shekara 28 bayan da ta kulla dangantakar da ba ta dace ba da wani dalibi dan shekara 17 a makarantar sakandare ta Riberbank a 2023, a cewar ’yan sandan Riverbank.

Malamar wacce take koyar da harshen Sipaniya tana aiki a makarantar tun 2016.

Haka kuma a cewar shafinta na LinkedIn, ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan kyau ga wani kamfani na kayan kwalliya.

A wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta ce, an fara gudanar da binciken ne bayan wani jami’in makarantar ya samu labarin alakar malamar da dalibin.

An kama Flores a cikin gidanta, inda aka tuhume ta da laifin yin lalata da karamin yaro ba bisa ka’ida ba, in ji ‘yan sanda.

Gundumar makarantar a baya ta bayyana wa jaridar The Modesto Bee cewa, za su hada kai da masu bincike idan akwai bukatar hakan kuma sun bai wa Flores hutu har sai an gama gudanar da bincike.

Mahukuntan makarantar sun ci gaba da cewa, za su yi magana da iyaye da daliban da suka yi rajista a azuzuwan Flores.

A cikin wata sanarwa, Sufeto Constantio Aguilar ya ce: ‘Abin takaici ne ga gundumarmu ta fuskanci yanayi irin wannan.

Yayin da muke ci gaba da yin aiki tare da jami’an tsaro, gundumar kuma za ta duba don tantance irin matakan da za ta iya bi don magance lamarin.’

Gundumar ta kara da cewa, ba ta tsammanin komai sai mafi kyawun inganci da kwarewar ma’aikatansu.’

An tsare Flores a gidan yari na Stanislaus County da neman beli a kan Dalar Amurka 20,000 bayan da wakilin gundumar suka samu sammacin kama ta.

Ofishin gundumar yankin Sheriff ya gode wa mahukuntar makarantar sabda ‘ba da rahoto cikin gaggawa’ da hadin kai wanda ‘ya taimaka wa masu bincike don tantance yanayin lamarin.’

Har yanzu dai ba a tabbatar da halin da take ciki a gidan yari ba. Babu tabbas ko Flores za ta daukaka kara.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka kama wani ma’aikacin makarantar sakandaren Riverbank da laifin yin lalata da wani dalibi ba.

A shekarar 2023 makarantar sakandare ta Riverbank ta fada cikin irin wannan yanayi bayan da aka zargi wani tsohon kocin kwallon kwando mai shekara 23 a lokacin da yin lalata da wani matashi dan shekara 16.

Logan Navors na fuskantar tuhumetuhume da suka shafi lalata da karamin yaro.

An gurfanar da Navors a gaban kotu a watan Satumba, amma ba a sani ba ko ya daukaka kara a wannan lokacin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa
  • Malaman Da Aka Dakatar 207, Sun Mika Takardar Neman Afuwa Ga Gwamnatin Zamfara
  • HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma
  • An kama malama tana lalata da ɗalibinta
  • Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi
  • Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC
  • Zargi: ’Yan sanda sun musanta sace tsohon Kwamishinan El-Rufai
  • Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar
  • Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya