EFCC ta kama Murja Kunya kan wulaƙanta takardun Naira
Published: 17th, March 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke shahararriyar jarumar nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.
Bayanai sun ce hukumar mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira.
NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru BauchiWata majiya daga EFCC ta tabbatar da cewa an kama Murja a ranar Asabar a Kano, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin, a cewar Gidan Rediyon Freedom da ke Kano.
Majiyar hukumar ta ce idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da ake zarginta da aikatawa.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Murja kimanin makonni uku da suka gabata, amma ta tsere daga beli kafin sake kama ta a ranar Asabar ɗin.
Murja Kunya ta yi kaurin suna tun bayan fara amfani da kafafen sada zumunta a matsayin abin barkwanci, kafin daga bisani ta mayar da shi dandalin sana’a.
A tsawon lokaci, ta shahara musamman a TikTok, inda take amfani da sunan “Yagayagamen,” duk da cewa a bayan nan ta jawo ce-ce-ku-ce a kanta.
A bayan nan dai hukumar ta EFCC ta cafke wasu abokan sana’ar Murja ’yan TikTok irinsu Alamin G-Fresh da Ashir Idris kan makamancin wannan zargi na wulaƙanta takardun kuɗi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano Murja Ibrahim Kunya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran titin Abuja zuwa Kano
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wadda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Da yake jawabi a taron kaddamarwar a Kagarko, Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya bayyana yadda aka yi watsi da hanyar da kuma irin mummunan tasirin da hakan ya yi ga rayuka da ci-gaban tattalin arziki.
Gwamna Uba Sani, ya yaba wa Tinubu bisa farfado da aikin, yana mai nuni da muhimmancin hanyar a matsayinta na mafi yawan zirga-zirgar ababen hawa a Arewa.
Da yake ba da tabbacin kamma aikin a cikin watanni 14, Tinubu wanda Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce za a gina titin ne da kankare, kamar babbar hanyar Legas zuwa Kalaba.
An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken TinubuMinistan ya kara da cewa aikin zan dangana har zuwa filin jirgin sama na Kano, kuma za a sanya kyamarorin CCTV gaba daya a tsawon titin, wanda sabon dan kwangila ne zai aiwatar.
Ya ce, shugaban kasa ya amince da naira biliyan 252 don muhimman sassan aikin, inda aka riga aka biya kashi 30%, yanan mai yaba muhimmiyar rawar da Gwamna Uba Sani ya taka a aikin.