Angola Ta Bukaci Tsagaita Wuta Kafin Taron Zaman Lafiya Tsakanin Kongo Demokradiyy Da Kungiyar M-23
Published: 17th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Angolan João Lourenço, wanda kuma shi ne ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya yi kira ga gwamnatin Congo Democradiyya da mayakn M-23 su kawo karshen yaki kafin taron tattauna batun tsagaita wuta a gabacin kongo nan gaba.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Afirca News” ya nakalto shugaban yana kira ga bangarorin biyu su tsagaita wuta da misalign tsakiyar daren jiya Lahadi don a tattauna batun samar da zaman lafiya cikin Nutsuwa.
Majiyar fadar shugaba Lourenco na cewa yakamata tsagaita wutan ya hada har da rashin kokarin mamayar karin iko a wasu wurare. Da kuma dakatar da fada. Da kashe fararen hula da sauransu.
An shiya cewa gwamnatin kongo Democradiyya da kuma wakilan yan tawayen M-23 zasu hadu a karon Farko don tattauna batun tsagaita budewa Juna wuta da kuma kawo karshen yakin a ranar 18 ga watan Maris, wato gobe talata , a birnin Luanda babban birnin kasar ta Angola.
Gwamnatin Kongo Democradiyya dai bata bayya a fili zata halarci taron sulhun wanda kasar Angola ta shirya ba, amma M-23 ta nuna goyon bayanta ga shirin na kasar Angola. Sai dai ta yikira ga shugaba Tsetsekedi ya bayyana anniyarsa ta zuwa taron sulhun a fili.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hisbah Ta Lalata Katan 51 Na Giya a Jihar Yobe
Ya ce shan giya yana barazana ga lafiyar jama’a tare da haddasa matsalolin zamantakewa.
A cewarsa, hana yaɗuwar giya zai rage aikata laifuka da kuma inganta zaman lafiya.
Dr. Yahuza ya kuma buƙaci al’umma da su mara wa Hisbah baya ta hanyar bayar da rahoto kan duk wani abu da ke saɓa wa doka.
Ya tabbatar da cewa hukumar ta ƙudiri aniyar ci gaba da aiki don tabbatar da adalci, zaman lafiya da gyara halayyar al’umma a Jihar Yobe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp