Kungiyar Ansarullah Ta Ce Keta Hurumin Kasar Da Amurka Ta Yi Zai Gamu Da Maida Martani
Published: 17th, March 2025 GMT
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa hare-haren ta’adanci wadanda sojojin Amurka da Burtaniya suka kai kan yankuna da dama a kasar ba zasu hana mutanen kasar ci gaba da kare Falasdinawa a Gaza ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Al-huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabata a jiya Lahadi da yamma.
Kafin haka dai jiragen saman yakin wadanda suka taso daga kan kataparen jirgin ruwa mai daukar Jiragen yaki na kasar Amurka sun kai hare hare a yankuna da dama a kasar ta Yemen wadanda suka hada da birnin San’a babban birnin kasar. Hare-haren dai sun kashe yara da mata da dama sannan sun lalata injunan wutan lantarki da dama.
Kungiyar Ansarullah ta kasar yemen dai ta tallafawa Falasdinawa a yankin tufanul Aksa wanda aka fara a ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023. Har zuwa lokacin da aka tsagaita wuta a ranar tsakanin Falasdinawa a Gaza da HKI a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025.
Amma a cikin yan makonnin da suka gabata HKI ta hana abinci da magunguna da kuma sauran bukatun Falasdinawa shiga yankin na Gaza. Wanda ya sa kungiyar ta koma tana hana jiragen HKI wucewa ta Tekun maliya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Habasha Ta Bukaci Kasashen Afirka Su Bunkasa Ciyar Yaki Da Cututtuka CDC Da Kungiyar
Firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya bukaci kungiyar tarayyar Afirka AU ta bunkasa aikin cibiyar yaki da cututtuka na kungiyar wato CDC don biyan bukatun kiwon lafiya na kasashen nahiyar gaba daya.
Kamfanin dillancin labaran Sputnic na kasar Rasha ya nakalto Abiy Ahmed yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da daraktan hukumar ta CDC a birnin Adis Ababa a ranar Jumma’an da ta gabata.
An kafa cibiyar yaki da cututtuka ta kungiyar tarayyar Afirka (CDC) ne, a shekara 2016, sannan ta fara aiki a shekara ta 2017 don kawo ci gaba a harkokin kiwon lafiyar a nahiyar Afirka.
Gwamnatin kasar China ce ta taimaka aka gina gine-gine cibiyar, aka kuma fara amfani da su a shekara ta 2023.
Abiy yace bunkasa cibiyar ta CDC zai taimakawa kasashen Afirka magance matsalolin kiwon lafiaya da dama a nahiyar.