CORET Za Ta Samar da Ayyuka 3,000 Ga Matasa A Jihohin Kaduna Da Jigawa
Published: 17th, March 2025 GMT
Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika wato CORET, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, sun bayyana shirinsu na samar da ayyuka guda dubu uku ga matasa ta hanyar sarrafa madara a sarkar darajar madara a Jahohin Kaduna da Jigawa.
Shugaban Shirin na CORET, Dr.
Taron horaswar na tsawon kwanaki biyu ya haɗa shugabanni daga ƙungiyoyin kiwo na madara guda goma sha biyu, masu tara madara, da shugabannin al’umma. Wannan shiri da ECOWAS ta ɗauki nauyi, zai fara aiki gwaje ne a ƙauyuka biyu, a Ladduga a Jihar Kaduna da kuma Maigatari a Jihar Jigawa.
Haka kuma, an samu goyon baya daga Hukumar Ci gaban Kasar Sweden, inda ake aiwatar da aikin ta hanyar haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi kamar Hukumar Kula da Makiyaya da kuma da sauran su.
Dr. Umar Hardo ya bayyana cewa taron horaswar na nufin bai wa ƙungiyoyin haɗin kai horo da ilimi a duk fannoni na samar da madara domin cigabansu
“CORET ta riga ta shiga haɗin gwiwa da kamfanoni irin su Milk Copal, Nestlé da Farm Fresh. Kuma an gina cibiyoyin tarin madara masu amfani da hasken rana a Ladduga da Maigatari,” in ji shi.
Dr. Umar Hardo ya ƙara da cewa an tsara horaswar ne akan matasa dari huɗu, amma matasa dari tara da ashirin da uku daga Ladduga suka nuna sha’awar shiga, lamarin da ya nuna yadda matasa ke da sha’awar shiga ƙungiyoyin haɗin gwiwa.
Ya ce daga cikinsu, an zaɓi matasa dari huɗu daga Maigatari, Jihar Jigawa don samun horo a cikin shirin.
“CORET ta sanya hannu kan yarjejeniya da Ma’aikatar Noma ta Tarayya da kuma Ma’aikatun Noma na Jihohin Kaduna da Jigawa domin aiwatar da wannan aiki,” in ji shi.
Shugaban Shirin ya bayyana cewa wannan wani babban cigaba ne a tarihin Najeriya, domin wannan ne karon farko da ake gina cibiyoyin tara madara masu na’urorin sanyaya madara domin sauƙin jigilar ta ba tare da ta lalace ba.
Ya ƙara da cewa wani sashi na shirin, shi ne gina cibiyoyin tara madara tare da horas da mahalarta a matsayin masu tara madara daga karkara waɗanda za su kula da wadannan cibiyoyi da kuma ƙungiyoyin haɗin ksn.
A cikin Kasidarshi, Tsohon Darakta na Raya Al’umma da Ƙungiyoyin Haɗin Kai a Jihar Kaduna, Mista Yohanna Kabirat, ya ce horon ya mayar da hankali ne kan ƙungiyoyin haɗin Kai da gudanarwa, da shugabanci domin su gudanar da ƙungiyoyinsu cikin nasara.
Ya jaddada muhimmancin ƙungiyoyin haɗin kai wajen ci gaba mai ɗorewa ga membobinsu, musamman matasa na Ladduga.
Mista Kabirat ya shawarci mahalarta su isar da ilimin da suka samu ga sauran membobinsu, musamman wajen yin bayanawa kowa bayyanai ba tareda an boye ba wanda shi ne babban kalubalen da ya jefa ƙungiyoyi da dama cikin matsalolin kudi a baya.
Tsohon Daraktan a karshe yace tushen nasarar kowace ƙungiyar haɗin Kai shine bin dokokin ƙungiyar yadda ya kamata.
Da suke magana da Radio Nigeria Kaduna, wasu daga cikin mahalarta taron, Sufyanu Umar da Fatima Isa, sun bayyana farin cikinsu da horon da aka basu, inda suka ce sun samu ƙwarewa ta musamman wajen tafiyar da ƙungiyoyinsu cikin nasara da inganci.
Mahalarta taron horaswar sun yaba wa CORET da sauran abokan ci gaba bisa shirya taron horaswar da suka ce zai sauya rayuwarsu ta fannin samar da madara.
Sun bayyana cewa ilimin da suka samu zai kasance ginshiƙi mai ɗorewa ga rayuwarsu da ci gabansu.
Rahoto daga Adamu Yusuf.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ayyuka Jigawa Samarda
এছাড়াও পড়ুন:
’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta
Wata ’yar kasar Jamus mai suna Alexandra Hildebrandt mai shekara 66 ta ja hankalin jama’a bayan ta haifi ɗanta na 10 ba tare da maganin haihuwa ba.
Haihuwar ta faru ne a ranar 19 ga Maris a Asibitin Charité da ke Berlin da taimakon likita.
Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a FilatoTa bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ta yi da Jaridar TODAY.com a ranar Laraba, 26 ga watan Maris.
A cewar Hildebrandt, ta rawa wa jaririn suna Philipp, wanda ya zo da nauyin kilo 7, kuma yana cikin koshin lafiya.
Ta bayyana shi a matsayin wanda ya dace da ’ya’yanta da ke da yawa, wanda ya haɗa da yara masu shekaru tsakanin 2 zuwa 46.
“Babban iyali ba kawai wani abu ne mai ban mamaki ba, amma duk da haka, yana da mahimmanci don renon yara yadda ya kamata,” in ji ta a cikin imel.
Hildebrandt, wanda ke kula da gidan tarihi na Wall Museum a Checkpoint Charlie a Berlin, ba bakon abu ba ne wajen jan hankalin jama’a.
Rayuwarta cike take da tarihi, domin zama uwa a wurinta abin mamaki ne.
Duk da shekarunta, ta nace cewa ciki ba a tsara shi ta hanyar kimiyya, amma ya faru ne ta dabi’a.
Mahaifiyar ta bayyana cewa, tana rayuwa cikin matukar aiki.
Kafin haihuwar Philipp, ta bayyana wa Jaridar Jamus ta Bild cewa, “Ina cin abinci cikin koshin lafiya, ina iya yin ninkaya tsawon awa guda a matsayin motsa jiki kuma ina tafiyar tsawon awa biyu.”
Likitanta, Dokta Wolfgang Henrich ya tabbatar da cewa, cikin nata ya daidaita, yana mai bayyana shi a matsayin cikin da ba shi da matsala sosai,” kodayake Hildebrandt ta yi haihuwa takwas a baya duk ta hanyar tiyata.
‘Ya’ayanta 10 sun hada da tagwaye, Elisabeth da Madimilian, dukansu shekarunsu 12, wadanda suke nuna cewa, rayuwar Hildebrandt a matsayin uwa cike take da matakai iri-iri.
Amma haihuwar ’ya’ya a irin waɗannan shekarun na tsufa ba kowa ba ne ke samun hakan.
Henrich ya yi gargaɗin cewa, masu juna biyu a shekarun tsufa na rayuwa cikin haɗari.
Ya bayyana cewa, “matsaloli irin su hawan jini da haihuwar jariri kafin mako 37 da kuma al’amurran da suka shafi zuciya da jijiyoyin jini yawanci na karuwa da shekaru”.
Ta ce, tana ta samun sakonnin taya murna da soyayya daga abokanta da danginta bayan sanar da haihuwar Philipp.
“Na yi ta samun sakonnin fatan alheri,” in ji ta TODAY.com.
A halin da ake ciki, masana kiwon lafiya sun yi imanin cewa, ba koyaushe shekaru suke taƙaita batun haihuwa ba.