Iran Ta Yaba Da Yarjeniyar Zaman Lafiya Da Aka Cimma Tsakanin Kasashen Armenia Da Azerbaijan
Published: 17th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya ba da sanya hannu a kan takardun yarjeniyar samar da zaman lafiya wanda kasashen Armenia da Azerbaijan suka yi. Ya kuma taya mutanen kasashen murmurnar wannan nasara.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana taya kasashen biyu murna a jiya lahadi, ya kuma kara da cewa, Iran a ko yauce tana fatan zaman lafiya a kasashe makobata da kasar sabuda dalilai da dama daga ciki Iran tana amfani da kasashe makobta don kyautata yanayin tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.
Firai ministan kasar Armenia Nikol Pashjinyan a zantawarsa ta wayar tarko da shugaban kasar Iran ya ce: Gwamnatinsa zata yi kokarin ganin an aiwatar da yarjeniyar daki daki kamar yadda aka tsara ta.
Kasashen biyu dai sun tabka manya-manyan yake yake a tsakaninsu, wadanda suka hada na shekara 1992 kan yankin Nagornu Karabal, sai kuma na shekara ta 2023 inda aka kashe mutane kimani 30,000 a tsakaninsu.
A shekara ta 2023 Azerbaijan ta kwace iko da yankin Nagorno Karabak wanda a dokokin kasa da kasa yankin Azerbaijan ne amma yan kabilar azari basu fi kasha 20% a yankin ba a yayin da sauran kuma Armeniyawa na. Kasashen biyu sun sami yanci ne a shekara 1991 bayan rushewar tarayyar Soviet.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Iran a shirye take ta shiga tattaunawa da Turawa bisa mutunta juna
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya nanata tsarin kasar na kulla kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da kasashen.
Iran da kasashen Turai dai na tattaunawar ba-zata kai a kai tun shekara ta 2021, shekaru uku bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar iran – tare da maido da takunkumin da Washington ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
bangarorin kasashen Turai da suka shiga yarjejeniyar nukiliya – Birtaniya, Faransa da Jamus – sun kasa cika alkawarin da suka dauka na dawo da Washington cikin yarjejeniyar.