HausaTv:
2025-03-17@14:21:33 GMT

Baka’i: Za Mu Mayar Da Martani Akan Wasikar Trump Bayan Yin Nazari

Published: 17th, March 2025 GMT

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya ce; Abinda ake watsawa a matsayin wasikar shugaban kasar Amurka shaci-fadi ne, domin har yanzu, mu ba mu watsa abinda ta kunsa ba.”

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai banbanci a tsakanin yadda Donald Trump yake Magana a fili da kuma abinda wasikar tasa ta kunsa.

Dr. Baka’i ya kuma kara da cewa; Bayan yin nazarin wasikar da abinda ta kunsa za mu bayar da jawabi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kore cewa ziyarar da ministan ma’aikatar tasu Abbas Arakci ya kai zuwa kasar Oman yana da alaka da bayar da jawabin wannan wasikar ta shugaban kasar Amurka.

Da yake mayar da jawabi akan harin da Amurka ta kai wa kasar Yemen, Dr. Baka’i ya ce abin takaici wannan ba shi ne karon farko da Amurkan ta kai wa Yemen hari ba, wanda shakka babu laifi ne kuma abin ayi Allawadai da shi ne.

Dr. Baka’i, ya  kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma kasashen musulmi da kungiyar kasashen ta musulmi da su dauki matakin gaggawa akan abinda yake faruwa.

Dangane da barazanar kai wa Iran hari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce; Duk wani wuce gona da iri akan Iran zai fuskanci mayar da martani mai tsanani ba tare da taraddudi ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ma aikatar harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

Yemen: Amurka Ta Sake Kai Wani Harin A Kasar Yemen

Kasar Yemen ta sanar da cewa Amurka da ta sake kai wasu hare-haren a gundumar Hudaidah akan wani kamfani na auduga.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto majiyar Ansarullah ta  kasar Yemen din tana cewa; Sojojin na Yemen sun kai hare-hare da makamai masu linzami har 18 akan jiragen ruwa na dakon jiragen yaki “USS Troman” hari.

Kakakin sojan kasar Yemen ne janar Yahya Sari ya sanar da kai hare-hare na martani akan jiragen yakin Amurka.

Tun daga ranar Asabar din da ta gabata ne dai jiragen yakin Amurka da na Birtaniya su ka rika kai wa Yemen hare-hare da sun yi sanadiyyar shahadar mutane da dama.

Yankunan da harin ya shafa sun hada biranen San’aa da kuma Sa’adah, sai kuma Hudaidai.

A gefe daya shugaban kungiyar Ansarullah ta Yemen Sayyid Abdulmalik Husi, ya ce: hare-haren ta’adanci wadanda sojojin Amurka da Burtaniya suka kai kan yankuna da dama a kasar ba za su hana mutanen kasar ci gaba da kare Falasdinawa a Gaza ba.

Haka nan kuma ya kara da cewa:  Za  su ci gaba da kai hare hare a kan jiragen HKI da na Burtaniya da na Amurkan, masu wucewa ta tekun malia kamar yadda ta bayyana tun farko.

Kungiyar Ansarullah ta kasar yemen dai ta tallafawa Falasdinawa a yakin tufanul Aksa wanda aka fara a ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023, har zuwa lokacin da aka tsagaita wuta tsakanin Falasdinawa a Gaza da HKI a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025.

Mayakan “Jubhatun-Nusrah’ Na Kasar Syria Sun Kai Hari Akan Iyakar Kasar Leabnon

A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon  ta yankin Hermul

Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar jami’an tsaro uku.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mayakan “Jubhatun-Nusrah’ Na Kasar Syria Sun Kai Hari Akan Iyakar Kasar Leabnon
  • Yemen: Amurka Ta Sake Kai Wani Harin A Kasar Yemen
  • IRGC: Iran ba za ta fara yaki ba amma za ta mayar da martani ga duk wata barazana
  • Abba ya mayar da filin Idi cibiyar harkokin addinin Musulunci
  • Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen JMI Ta Yi Allawadai Da Kungiyar G7 Wacce Ta Zargin Kasar Da Abubuwa Da Dama
  • Kungiyoyin Falasdinawa Suna  Cigaba Da Yin Allawadai Da Hare-haren Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen
  • Nageriya ta Maida Martani Kan Zargin Kissin Kiristoce A Kasar,Wanada Gwamnatin Amurka Ta Yi Mata
  • Amurka Ta Ce Bata Bukatar Jakadan Kasar Afirka Ta Kudu A Kasar, Bayan Da Ya Aibata Shugaba Trump