A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul

Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar jami’an tsaro uku.

Kungiyar ta Tahrirush-sham ta yi amfani da makamai rokoki da atalare  wajen kai hari daga kan iyaka.

Tuni dai kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta karyata zargin na kungiyar Tahrirus-sham.

Ofishin da yake kula da watsa labaru na Hizbullah ya bayyana cewa; Babu gaskiya a cikin labaran da ake watsawa na cewa Hizbullah tana da hannu a cikin abinda yake faruwa akan iyakar Lebanon da Syria.”

Sanarwar ta kuma kara da cewa; Muna sake jaddada cewa ba mu da alaka da duk wani abu da yake faruwa a cikin kasar Syria.

Wata kafa ta watsa labarai ta kasar Lebanon ta ce; kungiyar Agaji ta “Red Cross” ta mika gawawwakin wasu  mayakan kasar Syria su uku da aka kashe, ba tare da cikakken bayanin yadda aka kashe sub a.

Haka nan kuma majiyar ta bayyana cewa; an harba makamai masu linzami a cikin garin al-kasar da yake akan iyaka.

Ma’aikatar tsaron Syria ta sanar da kai hari da manyan bindigogi akan wasu garuruwa Lebanon da suke a kan iyaka.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda

Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita.

Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan rage farashin daga ₦880 da ta sayar a makon da ya gabata.

Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya

Hakan dai na nufin a cikin makonni shida, Dangoten ya rage farashin fetur ɗin sau uku.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • MDD Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Sake Raba Kasar Sudan Gida Biyu
  • Iran Ta Damu Akan Mummunan Yanayin Da Mutanen Al-Fasha Na Sudan Suke Ciki
  • WTO Ta Yi Gargadi Akan Karin Kudin Fito Na Amurka
  • Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda
  • Yadiot Ahranot: Amurka Ta Bayyana Lokacin Ficewarta Daga Syria
  •  ‘Yan Hamayyar Tanzaniya Sun Ki Amincewa Da Hana Su Shiga Zabe
  • Hamas Ta Fadawa Iyalan Yahudawan Da Take Tsare Dasu A Gaza Kan Cewa ‘Ya’yansu Zasu Koma A Cikin Akwatunan Gawaki
  • An Gudanar Da Taron Kasa da Kasa Don Tallafawa Yan Gudun Hijirar A Sudan
  • Ministan Harkokin Noma Na Kasar Iran Ya Kama Hanya Zuwa Kasar Brazil
  • Rundunar “Gulani” Ta Shiga Sahun Masu Kin Amincewa Da Yaki