Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara
Published: 17th, March 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Similanayi Fubara daga muƙaminsa.
Hakan na ƙunshe cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai cike da ƙorafi da majalisar ta fitar, inda take shirin tsige Gwamnan tare da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu.
Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumiA cikin wasiƙar wadda take kafa hujja ta tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya yi, ’yan majalisar sun zargin Gwamna Fubara da kashe kuɗaɗen jama’a ba bisa ƙa’ida ba.
Haka kuma, wasiƙar ta ce Gwamna Fubara ya hana majalisar gudanar da aikinta, da kuma naɗa mutane a muƙaman gwamnati ba tare da tantancewa ba.
Kazalika, tana tuhumar Gwamnan da ƙin biyan albashi da wasu alawus alawus da aka ware wa majalisar ciki har da dakatar da albashin Sakataren Majalisar, Emeka Amadi.
A bayan nan ne tsohon Gwamnan Ribas kuma Ministan Abuja mai ci, Nyesom Wike, ya ce ba zai hana majalisar sauke nauyin da rataya a wuyanta ba wajen tsige Gwamna Fubara.
A wata hira da manema labarai da ya gabatar ranar Laraba a Abuja, Mista Wike ya ce ’yan majalisar ba su yi laifi ba idan suka yanke shawarar tsige Fubara, saboda ya aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi, ciki kuwa har da riƙe musu albashi na tsawon watanni.
Aminiya ta ruwaito cewa, tun bayan ’yan watanni da zama Gwamnan Ribas, aka sa zare tsakanin Fubara da Wike, inda har kawo yanzu rikicin siyasa a tsakanin ɓangarorin biyu ke daɗa ƙamari.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dokokin Ribas Siminalayi Fubara Gwamna Fubara tsige Gwamna
এছাড়াও পড়ুন:
Idris Ya Musanta Rahoton Wai Ya Ce A Yi Watsi Da Koken Gwamna Zulum Kan Rashin Tsaro A Borno
Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce:
“E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba.
“Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare.
“Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci.
“Gwamnatin Tinubu tana da ƙwarin gwiwar kawar da ayyukan ‘yan bindiga da ta’addanci a faɗin ƙasar.
“Nasarorin da hukumomin tsaro suka samu a cikin watanni 18 da suka wuce suna nuna cewa lallai Nijeriya tana komawa daidai a hankali a hankali.
“Gwamnati tana kira ga kowa da kowa, musamman gwamnatocin jihohi, da su haɗa hannu wajen kawar da ragowar ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a duk inda suke.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp