Ba A Taɓa Shugaban Ƙasar Da Ya Kai Mahaifina A Nijeriya Ba – Ɗan Shugaba Tinubu
Published: 17th, March 2025 GMT
Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa mahaifinsa shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi, yana yaba wa shugabancinsa da himmarsa wajen bunkasa rayuwar matasa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana ranar Litinin, Seyi ya furta wannan magana yayin da yake jawabi ga taron matasa a jihar Adamawa.
Ya kara da cewa, “Shi ne kawai shugaban da ya kiyaye mutanenku a gida, tun lokacin da ya kasance gwamna har ya zama shugaban kasa. Shugaban da ya dauki matasa da muhimmanci, ya samar da dandali don matasa su zama wasu.” Seyi ya kuma bayyana cewa gwamnatin mahaifinsa tana kan kirkiro tattalin arzikin da zai amfanar da kowa, yana mai cewa, “Shi ne kawai shugaban da ba shi da nufin wadatar da kansa.”
Dalilin Da Ya Sa Tinubu Ya Nada Jega A Matsayin Mai Ba Shi Shawara Kan Samar Da Sauyin Noma Da Kiwo Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Karramawar Da Sojoji Suka Yi Wa Seyi TinubuKwanan nan, Seyi Tinubu ya shiga cikin ayyukan al’umma, musamman a jihohin arewacin Najeriya, inda aka gan shi yana rarraba kayayyakin abinci. A watan Maris, ya halarci wurare a jihar Kano, inda ya gana da mutane da dama ciki har da shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Hashimu Dugurawa, wajen buda bakin azumin Ramadan.
Haka kuma, Seyi ya ziyarci jihar Yobe a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinsa na shiga cikin al’umma da matasan Nijeriya. Ayyukansa na ziyartar jihohi da bayar da tallafi ga al’umma sun nuna kokarin da yake yi na kara kusantar jama’a da kuma tallafawa manufofin mahaifinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Legas Ya Koma APC Daga PDP
Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Legas na jam’iyyar PDP, Dr. Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya sanar da koma wa jam’iyyar APC mai mulki. Wannan sanarwar ta zo ne bayan kwanaki biyu kacal da ya fice daga jam’iyyar PDP.
Jandor ya ba da sanarwar koma wa jam’iyyar APC ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin yaƙin neman zaɓensa da ke Ikeja a ranar Litinin. Ya bayyana cewa ya yi shawarwari da shugaban ƙasa Bola Tinubu, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da wasu manyan mutane a fagen siyasa bayan ya fice daga PDP.
El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Haɗa Abokan Hamayya Don Yaƙar APC A Zaɓen 2027 Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – AtikuKakakin Jandor, Gbenga Ogunleye, ya tabbatar da cewa taron da ya yi da shugaban ƙasa ya gudana ne a ranar Litinin da ya gabata. Ya kuma bayyana cewa Jandor ya gana da wasu manyan shugabanni kamar tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Babangida, tsohon shugaban mulkin soja Abdusalami Abubakar, da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Prince Adewole Adebayo, domin yin shawarwari kan matakin da ya ɗauka.
Haka kuma, sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa da wasu shugabannin jam’iyyar sun ziyarce shi kwanan nan domin roƙonsa ya dakata kan matakin ficewa daga jam’iyyar. Duk da haka, Jandor ya ƙuduri aniyar ci gaba da shirye-shiryensa na siyasa a cikin jam’iyyar APC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp