Me Ya Sa Ba Za a Ba Yankin Taiwan Damar Samun ‘Yancin Kai Ba?
Published: 17th, March 2025 GMT
Sai dai hukumar yankin Taiwan na ci gaba da kokarin yada karairayi, tare da tunasar da kowa kasancewarta. In ba haka ba, wadannan bayanai masu kunshe da kurakurai da muka ambata ba za su bayyana a kan wata jaridar Najeriya ba. Hakika, a shekarun nan, hukumar Taiwan ta yi ta kokarin takala da batun neman “‘yancin kan Taiwan”, lamarin da ya haifar da mummunar barazana ga zaman lafiyar shiyyar da yankin ke ciki.
Tabbas za a tabbatar da dinkuwar kasar Sin waje guda. Yadda masu neman balle yankin Taiwan ke ta da zaune-tsaye ba zai haifar musu da da mai ido ba, illa sanya su gamuwa da ajalinsu cikin sauri. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
Hukumar kula da agaji ta MDD (OCHA) ta bada sanarwan cewa, gwamnatin HKI a yankin yamma da kogin Jordan ta kori Falasdinawa a gidaje 5 a yankin bayan sun rusa gidajensu. Hukumar ta kara da cewa wadanda HKI ta rusa gidajensu a yankin sun hada da yara 19 da da iyayensu 33 maza da mata 6.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto OCHA na cewa tun watan Maris da ya gabata zuwa yanzu, HKI ta rusa gidaje da gine-ginen Fafalsadinawa kimani 100 a yankin yamma da kogin Jordan wadanda suka hada da gabacin birnin Qudus da kuma sauran yankuna, da sunan an gina gidajen ba bisa ka’ida ba.
Banda haka suna kwace gonakin Falasdinawa don ginawa sabin yahudawan da suke shigowa kasar matsugunai.
Labarin y ace, a wasu lokutan yahudawan zasu tilastawa Falasdinawa rusa gidajensu da kansu ko kuma idan sun rusa su da kayan aikinsu su tilastawa Falasdinawan kbiyan kudaden aikin rusawan.