Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi
Published: 17th, March 2025 GMT
Bari ma in yi waiwaye. In yi bi-ta-da-ƙulli. Da jihohin Arewa na musulmi suke yin hutun lahadi ba su zuwa aiki to don su je gidan uban wane ne? A Katsina dai wannan ba zagi ne ba. A maye gurbinsa da hutun Juma’a ranar zuwa sallar Juma’a. Ranar Idi ce. Da ake yin hutu lokacin kirsimati ko wata Ista shi kuma hutun menene ne? Har yanzu Turawan na nan ne? Idan aka ce a yi hutu lokacin da yara ke taya iyayensu aiki a gona za su gane hikimar wannan tunda abinci zai zo gida.
A yi amfani da hutun a yi karatu, karatun ilmi na haƙiƙa. Da ‘yan bokon da ke mulki sun je makarantar Ramadan sun sauke kamar yadda suka je sakandare suka gama, wasu ma har sun je jami’a da ba su zama ɓarayi a ofis ba.
Da ba a riƙa tallata su a talabijin sun yi laya da biliyoyi ba. Da ba mu ga uba da dansa ba a gaban alkali ana cewa ku ɓarayi ne suna musu har lauyoyinsu na shedar zur. A sha ruwa lafiya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ba Don Tarbiyantar Da Mutane Nake Yin Fim Ba -Amina Shehu Lulu
Da ta ke amsa tambaya a kan rayuwa kafin samun daukaka da kuma bayan samun daukaka, Lulu ta amsa da cewar akwai banbanci sosai a rayuwata ta baya da kuma yanzu, saboda yanzu mutane da dama sun sanni ba kamar kafin in fara harkar fim ba, a wancan lokacin mutane basu damu da kai ba amma yanzu kuma ka samu masoya da wadanda ke ganin ba daidai kake yin abubuwa ba, saboda haka dole ne abubuwa su canza sosai.
Daga karshe jarumar ta ce ba ta fatan ace ta shafe shekaru fiye da goma a masana’antar ta nishadi, don kuwa ba ta son ace sai ta tsufa sannan za ta daina harkar fim, ina fatan ganin nan da shekara goma ace na koma gefe na baiwa matasa masu tasowa wuri domin kuwa bani son ace sai na tsufa a masana’antar kafin a daina dora mani na’urar daukar hoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp