Iran ta kuduri aniyar yin hadin gwiwa da hukumar IAEA
Published: 17th, March 2025 GMT
Iran ta bayyana anniyarta ta yin hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiya ta duniya IAEA.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi ya ce Tehran “na maida hankali” wajen hada kai da hukumar ta IAEA.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Gharibabadi ya yaba da tattaunawa mai ma’ana” da ya yi da Rafael Grossi, shugaban IAEA, a hedkwatar IAEA a Vienna.
Ya ce, bangarorin biyu sun tattauna batun hadin gwiwa tsakanin da warware batutuwan da ake takkadama, da batun tsaron cibiyoyin nukiliya, da sabbin batutuwan da suka shafi nukiliyar iran, da kuma dage takunkumi.
Jami’in na Iran ya kara da cewa dadadden hadin gwiwar dake tsakanin Iran da hukumar ta IAEA ya ba su damar warware ‘yan kadan daga cikin batutuwan da suke rage bambance-bambancen dake akwai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rayuwar ‘Yan Arewa Na Cikin Hadari, Yayin Da Gurbataccen Gishiri Ya Fantsama A Kasuwanni
Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama.
Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa.
Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da su a kanana wurare, ciki har da auna shi da abin da mazauna yankin ke kira ‘mudu’.
A manyan kasuwannin Kaduna da Maiduguri, kasuwar Sabon Gari da ke Sokoto, ana sayar da buhu mai nauyin kilogiram 25 a tsakanin Naira 46,000 zuwa Naira 50,000.
A cikin jaka mai nauyin kilo giram 25, ana iya samun kamar mudu ‘10 zuwa 15 ‘.
Abokan ciniki, ba tare da la’akari da hadarin dake tattare da kiwon lafiya ba, sun fi son wannan haramtaccen samfuri saboda yawan abin da za su samu daga mudu da kuma saukin yin almundahana ta hanyar cakuda shi da gishiri don kara yawansa da samun riba.
A kwanakin baya ne hukumar ta NAFDAC ta rufe wani dakin ajiyar kaya na kamfanin ‘DEE-LITE IMPED Distribution Co. Ltd’ da ke Jihar Sokoto, bayan ta gano wani adadi mai yawa na kayan abinci marasa rajista da suka hada da buhu 5,347 na MSG.
Rumbun ajiyar da ke kan titin Coca-Cola, daura da Western Bypass a Sokoto, an gano ya saba wa ka’idojin hukumar NAFDAC. A cewar hukumar ta NAFDAC, kamfanin ya shigo da haramtaccen samfurin MSG babu izini a karkashin takardar izinin sarrafawa amma an same shi yana sayar da samfurin kai tsaye, wanda haramun ne kuma yana da hadari ga lafiyar dan’Adam.
Wani masani kan harkokin kiwon lafiya da ke zaune a Gombe, Dokta Abdullahi Guruji ya ce ya kamata masu amfani da su su yi hattara da abubuwan da suke amfani da su domin gujewa duk wata matsala a fannin lafiya. Guruji ya ce ya zama wajibi masu amfani da su daina sadaukar da lafiyarsu a kan burin farashin kayan abinci masu arha.
A cewarsa, bai kamata a ce alhakin kare lafiyar mutum ya takaita ga hukumar NAFDAC da SON da sauran hukumomi kadai ba. Ya bukaci kowane dan Nijeriya da ya kula da kansa da kuma sauran ‘yan kasarsa domin kaucewa wannan hatsarin da ke kunno kai a harkar lafiya.
A yayin da yake kira ga masu sayar da abinci da su taka rawar gani a wannan fanni, ya bukace su da su kula da lafiyar kwastomominsu ta hanyar yin amfani da ingantattun kayayyakin dafa abinci.
Sai dai kwarare a fannin lafiyar ya dora wa hukumar ta NAFDAC alhakin kara kaimi a fannin tabbatar da doka da oda inda ya ce yin hakan zai dakile ayyukan marasa kishin Nijeriya da suke jajircewa wajen cutar da ‘yan Nijeriya.
“Duk lokacin da muka ziyarci kasuwa, za mu ceci mutane da yawa daga matsalolin kiwon lafiya ta hanyar rufe shagunan masu sayar da monosodium glutamate, masu sayar da magungunan jabu / marasa inganci, da masu siyar da abubuwan sha masu dandano, na cikin kwalba a cikin sauran abubuwan da ke zama abin sha,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp