Sojojin Sudan sun sanar da samun gagarumin ci gaba a tsakiyar Khartoum
Published: 17th, March 2025 GMT
Rundunar sojojin kasar Sudan (SAF) ta sanar da cewa, dakarunta sun samu ci gaba sosai a yakin da suke yi a babban birnin kasar Khartoum.
Mai magana da yawun rundunar sojin ta SAF, Nabil Abdalla ne ya fito fili ya bayyana cewa “Dakarunmu sun samu ci gaba sosai a tsakiyar birnin Khartoum.”
Sai dai kuma kungiyar ‘yan tawaye ta (RSF) ta musanta hakan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Siyo Tan Tan 360 Ga Manoma
Gwamnatin Jihar Jigawa ta siyo tan tan guda 360 domin tallafawa manoma don ci gaba da habbaka harkokin noma a Jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin noman rani na shinkafa a kauyen Jura dake Karamar Hukumar Auyo.
Ya yi bayanin cewar, gwamnatin ta kuma siyo injin girbin shinkafa guda 70 da sauran kayayyakin noma domin tallafawa manoman shinkafa.
A don haka, Gwamna Umar Namadi ya yi gargadin hukunta duk wanda aka samu ya karkatar da kayayyakin aikin gona da gwamnatin ta samarwa manoman jihar.
Yana mai cewar, fiye da manoma dubu hamsin da biyar ne za su amfana da shirin, wanda wani bangare ne na kokarin gwamnati na bunkasa aikin gona da wadata kasa da abinci.
Kazalika, Gwamnan ya kaddamar da rabon Babura 300 ga malaman gona domin wayar da kan manoma.
Ya kuma bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen bunkasa harkokin noma.
A cewar sa, wannan shirin yana daya daga cikin muhimman manufofi 12 da gwamnatinsa ta sanya a gaba, wadanda suke daidai da manufofin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na samar da wadataccen abinci ga ‘yan Najeriya.
Namadi ya bayyana cewar, tallafawa harkar noma da samar da malamai a fannin gona na daga cikin manyan hanyoyin cimma burin gwamnati na wadatar abinci da habaka tattalin arziki.
Ya kuma yaba da hadin kai da goyon bayan da manoma ke bayarwa wajen aiwatar da irin wadannan shirye-shiryen da gwamnati ke bullowa da su.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, kananan manoma za su samu rangwamen kashi 30 cikin 100, yayin matsakaita za su amfana da kashi 20, manyan manoma kuma za su samu kashi 10 akan kayayyakin da za su siya.
Kayayyakin da aka raba sun hada da injinan ban ruwa da takin zamani da magungunan kashe kwari da sauran su.
Usman Mohammed Zaria