Wasu manyan jami’an kasar Habasha sun bayyana cewa, layin dogon da ya sada tsakanin kasar Habasha da Djibouti da kasar Sin ta gina, yana kara inganta bangaren hada-hadar kayayyaki na kasar Habasha, kana ya zama wani muhimmin ginshiki da ke taimaka wa cinikayyar shigo da kaya da fitar da su zuwa kasashen waje a kasar.

Jami’an sun bayyana hakan ne a wata ganawa da suka yi tare da masu ruwa da tsaki a harkar sufuri da shigo da kayayyaki da fitar da su waje na kasar Habasha, a ranar Asabar da ta gabata.

Da yake jawabi a wajen taron, ministan sufuri da hada-hadar kayayyaki na kasar Habasha, Alemu Sime ya bayyana cewa, kasar da ke gabashin Afirka tana aiki tukuru don zamanantar da fannin sufuri da hada-hadar kayayyaki, a wani bangare na burin da ta sa a gaba wajen kawo sauyi ga harkokin cinikayyar shigo da kayayyaki da fitar da su waje.

Ya ce, layin dogo da ya sada tsakanin kasar Habasha da Djibouti mai tsawon kilomita 752, yana kara kaimin tabbatar da cikar burin kasar, yana mai bayyana muhimmancin ingantawa da fadada samar da harkokin sufurin ababen hawa da kayayyaki, tare da mayar da hankali musamman a kan layukan dogo. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: hadar kayayyaki kasar Habasha

এছাড়াও পড়ুন:

 Rasamani: Asarar Yakin HKI Ta Kai Dalar Amurka Biliyan 14

Ministan ayyuka da sufuri na kasar Lebanon Yusuf Rasamani ya bayyana cewa; Asarar da HKI ta jazawa kasar Lebanon a lokacin yaki ta kai dalar Amurka biliyan 14, tare da bayyana cewa kasar Rasha ta bijiro da cewa za ta taimaka.

Rasamani ya fada wa Radiyon “Sputnik” na Rasha cewa; Suna ci gaba da aiki tare da babban bankin duniya, domin tantance barnar da yakin Isra’ila ya haddasa a Lebanon.”

Bugu da kari ministan ayyukan na kasar Lebanon ya kuma ce; Ma’aikatar ta fara aikin debe baraguzai a cikin garuurwan da za su iya isa, wadanda babu sojojin HKI a cikinsu.”

Haka nan kuma ya ce; Kasar ta Lebanon da kuma Bankin Duniya da Asusun bayar da Lamuni suna aiki domin fito da tsarin aiki na sake gina wuraren da yakin ya rusa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya
  • Tattalin Arzikin Al’Ummar Kasar Sin Na Tafiya Yadda Ya Kamata A Watan Jarairu Da Fabrairu
  • Kasar Habasha Ta Bukaci Kasashen Afirka Su Bunkasa Ciyar Yaki Da Cututtuka CDC Da Kungiyar
  • Ramadan Iftar: Sarkin Kauru Ya Hori Al’umma Su Hada Kai Su Zauna Lafiya da Juna
  • Gwamnatin Trump na tunanin hana ‘yan kasashe kusan 40 ciki har da Iran shiga Amurka
  • Kasar Sin Na Adawa Da Zarge-Zargen G7 Don Gane Da Tekun Kudancin Kasar
  •  Rasamani: Asarar Yakin HKI Ta Kai Dalar Amurka Biliyan 14
  • Fitar Da Nama Zuwa Saudiyya: Mayankar Dabbobi Ta Jurassic Ta Yi Hadin-gwiwa Da Shirin CDI
  • Majalisa Ta Bukaci CBN Ya Gaggauta Dakatar Da Karin Caji A ATM