Leadership News Hausa:
2025-04-13@14:29:43 GMT

Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya

Published: 17th, March 2025 GMT

Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya

A ranar Larabar da ta gabata ne, harajin kashi 25 na shugaban Amurka Donald Trump kan duk wasu kayayyakin karafa da goron ruwa ya fara aiki. Inda Kanada ta mayar da martani kai tsaye da harajin kashi 25 kan kayayyakin Amurka na sama da dala biliyan 20, wadanda suka hada da karafa, kwamfutoci da kayan wasanni.

EU ita ma mayar da martani da haraji kan kayayyakin Amurka na kusan dala biliyan 28, wanda zai fara aiki a ranar 13 ga Afrilu.

Hasashen dake tattare da manufar Trump shi ne, idan farashin kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje ya tashi a dalilin karin haraji, to za a maida hankali kan kafa masana’antun cikin gida dake samar da irin wadannan kayayyaki, ta hakan za a samu karin ayyukan yi a Amurka. Sai dai Trump ya manta cewa, tsarin karin harjin kwastam na iya zama takobi mai kaifi biyu idan aka yi amfani da shi ba bisa ka’ida ba, kuma zai iya raunata wanda ke rike da shi. Wannan takobin a hannun Trump, yana barazanar zama “makamin lalata huldar cinikayya tsakanin kasa da kasa,” yayin da hakan ke mummunan tasiri ga tattalin arzikin Amurka.

Layin Dogo Na Habasha-Djibouti Na Habaka Kasuwanci Da Karfafa Hada-hadar Kayayyaki  Gwamnatin Kano Ta Umarci Ma’aikatanta Da Su Tantance Allbashin Watan Maris Kafin A Biya Su

Sanin kowa ne cewa Amurka ba za ta iya farfado da tsarin samar da kayayyaki da masana’antunta da suka dade da bacewa a cikin dare guda ba, zai dauki watanni ko ma shekaru kafin a sake fasalin tsarin samar da kayayyaki da masana’antunta, duk da cewa masu sayayya na Amurka sun riga sun tsunduma cikin matsalar hauhawar farashin kayayyaki na yau da kullum, sakamakon matakin kara haraji na Trump.

Bisa ka’ida, Trump yana da shekaru hudu ya cimma manufarsa, amma a aikace, lokacin ya yi kadan da zai gamsar da masu sayayya na Amurka. Idan har wannan manufar ta ci gaba da kasancewa a cikin watanni masu zuwa, to tabbas jama’a za su janye goyon bayansu ga shugaban, hatta a tsakanin ‘yan jam’iyyar Republican Congress, wadanda ya dogara da su wajen aiwatar da sabbin dokoki. Idan har suna ganin damar saken zabarsu na cikin hadari a zaben tsakiyar wa’adi na badi saboda tsarin tsuke bakin aljihu da matakin kara kudin fito da ya aiwatar, za su iya yin watsi da goyon bayan da suke baiwa shirin shugaban kasar. Tuni dai ana samun karuwar damuwa daga ’yan kasuwa, musamman wadanda suka dogara da tsarin samar da kayayyaki na duniya wanda manufar kudin fito ta Trump ta kawo ma cikas. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa

Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima.

“Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.”

“Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.”

Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.”

Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin Tinubu, wanda ke da nufin zurfafa rikon amana da inganta ayyukan yi a dukkan matakan gwamnati.

Daga cikin muhimman sauye-sauyen, Shettima ya bayyana yunkurin samar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi a matsayin muhimmin abu wajen kusantar da mulki ga jama’a.

Ya yaba da sanarwar da Kotun Koli ta yi a baya-bayan nan da ke tabbatar da wannan ‘yancin cin gashin kai, yana mai bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na gina tarayya mai aiki.

Da yake buga misalai da wasu kasashe irin su Canada, Jamus, da Spanya, Shettima ya yi gargadi game da nuna son kai ga tsarin kasashen waje, da masu ruwa da tsaki da su bi tsarin tarayyar Nijeriya na musamman wanda ya samo asali daga rikon amana, tattaunawa da ci gaban kasa.

“Babu wani tsarin wata kasa da za a ce bai da matsala. Kowace gwamnati tana tasowa ne sannu a hankali,” in ji shi. “Dole ne mu yi tsayin daka wajen ganin mun sauka daga hanyoyin da aka shigo da su daga waje wadanda suka gaza yin la’akari da irin bambancin zamantakewarmu, kabilanci, da kuma yawan al’ummar mu.

“Abin da ya fi damun ‘yan Nijeriya na yau da kullun ba shi ne ka’idar tsarin tarayya ba, amma shin mulki yana samar da ruwa, wutar lantarki, makarantu, hanyoyi, da asibitoci ?,” in ji Mataimakin Shugaban.

Ya amince da tsauraran matakan kasafin kudi na gwamnati, gami da cire tallafin mai da gabatar da sauye-sauyen haraji – kamar yadda ya dace don gina gwamnati mai cikakken iko.

Shettima ya kuma taya wadanda suka samu lambar yabon murna, inda ya kira karrama su da “Bikin murna da himmar zuwa ga karin aiki” tare da karfafa musu gwiwa wajen nuna gaskiya a harkokinsu.

 

Dole Ne Mu Karfafa Tsarinmu Tafi Da Gwamnatinmu – Gwamna Namadi

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi daya daga cikin wadanda suka karbi lambar yabo ta LEADERSHIP, ya jaddada bukatar karfafa tsarin kasafin kudin tarayyar Nijeriya.

Namadi, wanda ya yi magana bayan karbar kyautar Gwarzon Gwamnan na Shekara, ya bayyana kyautar a matsayin “abin burgewa da girmamawa.

Ya lura cewa taken taron ya dace sosai kuma an yi shi a kan lokaci.

“Na yi imani zai ba da gudummawa wajen tattaunawa a game da bangarori daban-daban na gyare-gyaren kasafin kudi da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a karkashin tsarin sabunta abin da ake fata,” in ji shi.

Gwamnan na Jigawa ya kara da cewa tattaunawar da ta shafi kudurin dokar sake fasalin haraji da ke gaban majalisar wadda za ta ba da gudummawa ga kokarin karfafa tsarin tarayya na kasafin kudin Nijeriya.

Da yake yaba wa shirin ba da lambar yabo na LEADERSHIP, gwamnan ya ce, “Za mu ci gaba da himma wajen kwadayin sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasar ya dora mana, tun da muka karbi ragamar mulki, burinmu shi ne mu sauke nauyin da aka dora mana bisa gaskiya da hangen nesa na Jihar Jigawa.

“Saboda haka, za mu mai da hankali da yin tsayin daka kan kudurinmu na ci gaba da inganta zamantakewar al’ummarmu cikin himma da kuma hada kai ga jihar Jigawa mai girma na yanzu da kuma nan gaba,” in ji shi.

 

Za Mu Tabbatar Da Cewa Dukkan Yaranmu Suna Makaranta – Gwamnan Kano

Haka shima Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, wanda aka karrama shi da lambar yabo, ya yi alkawarin tabbatar da cewa sai sun yi duk mai yiwuwa wajen ganin yaran Kano da ba sa zuwa makaranta sun koma makaranta.

Ya kuma sadaukar da lambar yabon da aka bashi ta Gwarzon Gwamnansa ga yara marasa galihu a fadin kasar nan.

 

Ba Za Mu Tauye Hakkin ‘Yan Jarida Ba – AGF

A nasa bangaren, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Cif Lateef Fagbemi, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ba ta tauye hakkin ‘yan jarida.

Ya bayyana cewa kasancewarsa a wajen taron wata bayyananniyar sanarwa ce daga gwamnatin Tinubu kan kare ‘yancin ‘yan jarida.

“Bayan ‘yan shekaru bayan da aka kafa kamfanin, an samar da tsari mai ban mamaki game da taka muhimmiyar rawa a fadin jihohi da sassa, wanda ya ba mu damar girmama wadanda ke ba da gudummawa ga ci gaban kasa,” in ji shi.

Fagbemi ya taya shuwagabannin LEADERSHIP da ma’aikatansa murna kan kokarin da suke yi da kirkire-kirkire kuma ya yi addu’a ga wanda ya kafa jaridar.

“Ina taya wadanda aka karrama murna; wannan karramawa ya kamata ya zama kalubale ga wadanda ake jagoranta da za su a bayanmu,” in ji shi.

Ya kara da cewa ya kamata a karrama daidaikun mutane a lokacin rayuwarsu, yana mai jaddada cewa karramawar wani karamci ne ga kasa.

Ya kara da cewa “Wannan karramawa wani abu ne na farin ciki da na sanya shi a raina, ina matukar farin cikin wannan karramawa da aka yi mana tare da takwarorina uku na majalisar zartarwa ta tarayya da wasu manyan mutane daga wasu sassa.”

Da yake zanta da jigon taron, Fagbemi ya bayyana jin dadinsa da yadda aka mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi kasa baki daya, inda ya ce, “Batun tsarin tarayya, wanda ya hada da kalubale, da damammaki, yana da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa.”

Ya kara jaddada goyon bayansa ga manema labarai, yana mai cewa, “Kasancewata a matsayina na babban lauya a wannan taron, wata shaida ce ga irin sadaukarwar da tarayyar Nijeriya ta yi na ‘yancin yada labarai a karkashin ingantacciyar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

 

Muna Fatan Karramaswar Za Ta Zaburar Da Wadanda Suka Samu – Zainab Nda-Isaiah

Ita ma da take gabatar da nata jawabin, shugabar kamfanin LEADERSHIP, Misis Zainab Nda-Isaiah, ta yi kira da a sauya yadda ake gudanar da bukukuwa masu nagarta a Nijeriya, inda ta ce karramawar da aka yi wa ‘yan kasa ya kamata ta kasance a matsayin abar amincewa da samun nasara da kuma zaburarwa gami da kara himma.

Da take jawabi a wajen taron LEADERSHIP da bayar da kyaututtuka, a jiya, Misis Nda-Isaiah ta ce bikin ba wai an shirya shi ne domin yabo kawai ba, a a har ma da kokarin samar da wani gagarumin tasiri ga ‘yan kasa.

“Ba kawai ya taron ya ta’allaka ne kan bayar da kyaututtuka da yabo kadai ba,” in ji ta. “Ya kamata taron ya zama fiye da haka, ya kasance yana zaburar da da al’umma, musamman a cikin wannan hali na matsanancin tattalin arzikin duniya, inda hannu baka-hannu karya ya zama al’ada.”

Misis Nda-Isaiah ta yaba wa marigayi mijinta wanda ya kafa kamfanin a 2004 Sam Nda-Isaiah, bisa hangen nesa mai tushe a cikin hidima da kishin kasa.

“Shekaru 20 da suka gabata, shugabanmu wanda ya kafa wannan kamfani ya tsunduma harkar jaridu da kaifin basira inda ya bashi taken- Domin Allah da Kishin Kasa. Wannan hangen nesa ya ci gaba da yi mana jagora, kuma da yardar Allah zai dore har zuwa zamani masu zuwa,” in ji ta.

Ta bayyana bikin a matsayin wani lokaci na karrama nasarorin da aka samu a bana da kuma kalubalantar kowane dan Nijeriya da ya yi tunani kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen gina kasa.

“Wadannan fitattun shugabanni, kowane mai bin diddigi ne a cikinsu, yana tunatar da mu ganin ikon manya, ra’ayoyi, juriya, da tausayi. Suna karfafa mana gwiwa wajen kawo sauyi, wani bambanci wanda ke nufin tallafa wa mutane da yawa da kuma gudunmawar da ke inganta rayuwa a cikin al’ummomi.”

“Yayin da muke biki don wadanda aka karrama a yau, kowannenmu yana da damar zama mai kawo sauyi. Za mu ci gaba da zaburar da juna,” in ji ta.

 

Jawabin Godiya Daga Shugaban Editoci

Babban Mataimakin Shugaban Kamfanin LEADERSHIP, Mista Azu Ishiekwene, ya mika godiyarsa ga wadanda suka yi nasara, abokan huldar kasuwanci, masu tallafawa, da kuma ‘yan kwamitin ba da shawara kan gudummawar da suka bayar.

Ya kuma gode wa wakilin mataimakin shugaban kasa, da duk wanda ya yi aiki a bayan fage, da ma’aikatan fadar shugaban bisa goyon bayan da suka bayar.

“Yayin da muke kammala wannan taro a wannan rana mai ban mamaki, Ina so in rufe da wata kalma da daga Mahatma Gandhi. Inda ya ce: ‘Hanya mafi kyau da za ku ‘yanta kanku ita ku tabbata cikin yi wa wasu hidima”.

“A yau, muna bikin wadanda suka tabbatar da kansu a cikin hidimarsu, kuma sun sami daukaka, muna godiya ga wadanda suka yi nasara wadanda suka zaburar da mu, abokan kasuwancinmu da masu daukar nauyi gami da masu goyon bayanmu, da kuma mambobin kwamitinmu na ba da shawara da suka ci gaba da raka mu.

“Ga masu sauraronmu daga nesa da na kusa, gami da masu kallon mu ta wasu hanyoyi, kuma wani bangare ne na tafiyarmu, muna yi muku godiya.”

Ishiekwene ya mika godiyarsa ga ministan Babban Birnin Tarayya, da sauran ministoci da gwamnoni, shugabannin masana’antu, shugabannin kungiyoyin farar hula, da mambobin ‘Fourth estate of The Realm’ da suka yi hakurin gudanar da shirin, ciki har da wakilai.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar
  • Za A Samar Da Ababen Hawa Ga Malaman Sakandare A Jigawa
  • Axios: Makomar Tsarin Jarin Hujja A Duniya  Tana Girgiza
  • Iyaye Mata Sun Bukaci A Rika Samar Da Kayayyakin Bada Tazarar Haihuwa Akan Lokaci
  • Amurka Ta Sayi Kayayyakin Nijeriya Na Dala Miliyan 643 A Wata 2 – Rahoto
  • Iran: Akwai damammaki na diflomasiyya da za mu jarraba aniyar Amurka a kansu
  • Masarautar Kauru Ta Bayyana Rashin Sha’awarta Kan Shiga Sabuwar Jihar Gurara
  • Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
  • Karin Harajin Amurka: Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya
  • E.U.  ta dauki wasu sabbin matakan kalubalantar harajin fito na Amurka