Atisayen Soji A Mashigin Tekun Taiwan Babban Gargadi Ne Ga ‘Yan Awaren Taiwan
Published: 18th, March 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Litinin cewa, atisayen da sojojin kasar Sin suka yi a mashigin tekun Taiwan wani muhimmin martani ne ga goyon bayan da kasashen waje ke nunawa kan yunkurin neman “’yancin kan Taiwan,” kuma babban gargadi ne ga ‘yan awaren Taiwan.
Kakakin ta ce, matakin soja da kasar Sin ta dauka ya wajaba, kuma yana bisa doka, ya kuma dace don kare ikon mallakar kasa, da tsaro da kuma cikakkun yankunanta.
Mao ta bayyana hakan ne a lokacin da take ba da amsa ga tambayoyi a taron manema labarai na yau, inda ta ce, rahotanni sun nuna cewa, sojojin kasar Sin sun gudanar da atisayen soji a mashigin tekun Taiwan a yau Litinin. Kuma an yi imanin cewa, atisayen na da nasaba da sauye-sauyen da aka yi a shafin yanar gizon ma’aikatar harkokin wajen Amurka a baya-bayan nan dangane da manufar Taiwan, da kuma ayyukan ‘yan aware masu neman ‘yancin kan Taiwan. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Rasamani: Asarar Yakin HKI Ta Kai Dalar Amurka Biliyan 14
Ministan ayyuka da sufuri na kasar Lebanon Yusuf Rasamani ya bayyana cewa; Asarar da HKI ta jazawa kasar Lebanon a lokacin yaki ta kai dalar Amurka biliyan 14, tare da bayyana cewa kasar Rasha ta bijiro da cewa za ta taimaka.
Rasamani ya fada wa Radiyon “Sputnik” na Rasha cewa; Suna ci gaba da aiki tare da babban bankin duniya, domin tantance barnar da yakin Isra’ila ya haddasa a Lebanon.”
Bugu da kari ministan ayyukan na kasar Lebanon ya kuma ce; Ma’aikatar ta fara aikin debe baraguzai a cikin garuurwan da za su iya isa, wadanda babu sojojin HKI a cikinsu.”
Haka nan kuma ya ce; Kasar ta Lebanon da kuma Bankin Duniya da Asusun bayar da Lamuni suna aiki domin fito da tsarin aiki na sake gina wuraren da yakin ya rusa.