Kokarin Kasar Sin Na Bunkasa Hadin Gwiwar Neman Ci Gaban Duniya Na Nan Daram
Published: 18th, March 2025 GMT
Kakakin hukumar raya hadin gwiwar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin (CIDCA), Li Ming, ya bayyana a gun taron manema labaru na yau Litinin cewa, rage yawan tallafin kasashen waje da Amurka ta yi, da rage fiye da kashi 90 cikin 100 na ayyukan da take yi, sun sabawa alkawuran da ta dauka, da kuma nauyin da ke bisa wuyanta a karkashin tsarin MDD, kuma hakan wani yunkuri ne na ja da baya, wanda kasashen duniya ba sa goyon baya.
Li Ming ya jaddada cewa, alkawarin da kasar Sin ta yi na kara yawan albarkatu ga hadin gwiwar ci gaban duniya, ba zai canza ba. Ya kara da cewa, ka’idojin kasar Sin na kin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu, da kin sanya sharadi na siyasa, da kin yin alkawuran banza suna nan daram. Ban da wannan kuma, yadda kasar Sin ke bin tsarin ba da tallafi na ketare bisa gaskiya da rikon amana, da kudurinta na yin shawarwari bisa daidaito da hadin gwiwar samun nasara tare da kasashe masu ci gaba da masu tasowa ba za su canza ba.
Li Ming ya ci gaba da cewa, dole ne kasashen da suka ci gaba su tabbatar da bin ra’ayin bangarori daban daban bisa gaskiya, da mutunta alkawuransu na tabbatar da ci gaba, da nuna sanin ya kamata, da yin watsi da dabarun tashin wani faduwar wani, da hada kai da kasashe masu tasowa, don ci gaba da aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD ta shekarar 2030, da gina al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Habasha Ta Bukaci Kasashen Afirka Su Bunkasa Ciyar Yaki Da Cututtuka CDC Da Kungiyar
Firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya bukaci kungiyar tarayyar Afirka AU ta bunkasa aikin cibiyar yaki da cututtuka na kungiyar wato CDC don biyan bukatun kiwon lafiya na kasashen nahiyar gaba daya.
Kamfanin dillancin labaran Sputnic na kasar Rasha ya nakalto Abiy Ahmed yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da daraktan hukumar ta CDC a birnin Adis Ababa a ranar Jumma’an da ta gabata.
An kafa cibiyar yaki da cututtuka ta kungiyar tarayyar Afirka (CDC) ne, a shekara 2016, sannan ta fara aiki a shekara ta 2017 don kawo ci gaba a harkokin kiwon lafiyar a nahiyar Afirka.
Gwamnatin kasar China ce ta taimaka aka gina gine-gine cibiyar, aka kuma fara amfani da su a shekara ta 2023.
Abiy yace bunkasa cibiyar ta CDC zai taimakawa kasashen Afirka magance matsalolin kiwon lafiaya da dama a nahiyar.