Iran An Dauke Wa Mahdi Karubi Daurin Talalar Da Aka Yi Masa A Gida
Published: 18th, March 2025 GMT
Dan Mahadi Karubi, wanda yana ya jagoranci boren 2009 bayan zaben shugaban kasa, ya bayyana cewa an daukewa mahaifin nashi daurin talalar da aka yi masa bisa umarnin ma’aikatar sharia.
Shi dai Mahadi Karubi an yi masa daurin zaman gidan ne bayan hargitsin da ya jagoranta bayan zaben shugaban kasar da aka yi a 2009.
Husain Karubi ya fada wa kamfanin dillancin labarun “IRNA” cewa; An fada wa mahaifina cewa, Daga nan zuwa watan Aprilu zai iya gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum ba tare da kaidi ba, amma daga yanzu zuwa lokacin zai iya sanar da jami’an tsaro inda yake son zuwa gabanin kwana daya.
Harigitsin day a biyo bayan zaben 2009 a Iran wanda ‘yan takara uku fitattu su ka tsaya, da su ne Ahmadinejad da ya lashe zaben, sai kuma Mirhusain Musawi da Mahdi Karubi. Wadanda ba su ci zaben ba, sun riya cewa an yi magudi a zaben, lamarin da mahukunta su ka kure shi saboda rashin wani dalili da madogara.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Newcastle Na Gab Da Samun Gurbi A Gasar Zakarun Turai
Newcastle ta lallasa Leicester da ci 3-0 a ranar Litinin a gasar Firimiya Lig ta Kasar Ingila, wasan wanda ya kasance na 8 a jere da Leicester City ta buga ba tareda jefa kwallo a raga ba, Newcastle da Eddie Howe ke jagoranta na fatan ganin sun samu gurbi a gasar Zakarun Turai na badi, tun da farko dai sun lashe gasar League Cup a watan da ya gabata.
Yanzu haka su na matsayi na biyar a kan teburin Firimiya, inda suke da maki daya da Chelsea da ta ke matsayi na hudu, Leicester City kuma a nata bangaren ka iya komawa gasar ‘yan dagaji ta Championship idan aka doke su a wasansu na gaba a gasar.
Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar KayaNewcastle, wacce arzikinta ya bunkasa tun bayan da mamallakanta ‘yan Kasar Saudiyya su ka karbi iko a shekarar 2021, ta na neman sake samun damar buga gasar Zakarun Turai tun bayan wanda aka kore ta a shekarar 2023/24 bayan shafe shekaru ashirin.
Howe, wanda ya jagoranci Newcastle lashe babban kofi na farko cikin shekaru 56 a wasan da su ka doke Liverpool a Wembley a watan da ya gabata, ya na da damar kara haskakawa a wannan kakar wasanni ta bana mai dimbin tarihi a wajen Newcastle.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp