Fizishkiyan: Addinin Musulunci Da Kur’ani Mai Girma Suna Tabbatar Da Shimfida Adalci
Published: 18th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Dukkanin batutuwan da Musulunci da kuma al’kur’ani maigirma suke bijiro da su, sun ginu ne akan ginshikin gaskiya da kuma adalci.
Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Idan har wadannan ginshikan biyu su ka zama ana aiki da su a cikin al’umma, to za a sami shiriya.
Shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce; A wannan lokacin muna da bukatuwa da koyar da dalibai da ‘ya’yanmu domin su kai ga mataki na koli na ilimi da kuma kyawawan halaye, ta yadda za su zama karfin madogara da hikima da kyawawan halaye a cikin al’umma.
Shugaban na kasar Iran ya kuma ce: Abubuwan da musulunci da kuma al’kur’ani suke bijiro da su, sun ginu ne akan ginshikai biyu da su ne gaskiya da kuma adalci a cikin dukkanin fagage.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana cewa; Tun cin nasarar juyin musulunci, Iran ta zabi hanyar tattaunawa, saboda ta tabbatar da kyakkyawar niyyarta da kuma aiki da hankali a mu’amalrta da duniya.
Limamin na Tehran Ayatullah Saiddiki ya ce, a yayin tattaunawar da za a yi a tsakanin Iran da Amurka wacce za ta kasance ta hanyar shiga tsakani, Iran za ta ji abinda daya bangaren zai fada, sannan kuma ta bayar da jawabi, domin tabbatarwa da duniya cewa ita daula ce mai aiki da hankali, kuma ba ta tsoron tattaunawa.
Ayatullah Siddiki ya yi ishara da zancen jagoran juyin musulunci akan yadda bangaren da ake tattaunawar ba ya aiki da abubuwan da aka cimmawa da amincewa da su.
Haka nan kuma limamin na Tehran ya ambato jagoran juyin musuluncin na Iran yana bayyana yadda Amurka take kiyayya da Jamhuriyar da musulunci na Iran da addinin musulunci da kuma alkur’ani mai girma, saboda asarar manufofinta da ta yi a cikin Iran.
Ayatullah Siddiki ya kuma amabci cewa maganar da shugaban kasar Amurka yake yi na tattaunawa kai tsaye da Iran ba koma ba ne, sai yaudara da ba ta da tushe. Kuma saboda yadda Amurka ba ta aiki da duk wata yarjejeniya da aka cimmawa, don haka zama da ita gaba da gaba domin tattaunawa bai dace da mu ba.
Har ila yau, ya kuma ce, Shirin Iran na Nukiliya na zaman lafiya yana ci gaba da samun bunkasa saboda jagoranci na hikima na jagoran juyin juya halin musulunci.