Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi ya bayyana cewa; Matukar Amurka ta ci gaba da kai wa Yemen hare-hare, to suna da hanyoyi da za su iya gasa mata aya a hannu masu yawa.

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishara da yadda dubun dubatar mutanen Yemen su ka fito a cikin birnin San’aa da kuma sauran biranen kasar domin raya da tunawa da rana da aka yi yakin Badar, yana mai cea; hakan yana a matsayin wani sako ne zuwa Amurka da Isra’ila, kuma tabbas idan su ka ci gaba da kai wa Yemen hari, to muna da zabi na  hanyoyin da za mu yi amfani da su domin dandana musu kudarsu.

 Sayyid Husi wanda ya gabatar da jawabin dararen Ramadan mai alfarma ya kara da cewa; Sakon mutanen Yemen da su ka fito a Litinin din nan 17 ga watan Ramadana shi ne; Ba za mu taba barin abokan gaba Isra’ilawa su ci gaba da cutar da al’ummar Falasdinu, a karkashin goyon bayan Amurka ba.”

Shugaban na Ansarullah ya kuma yi Magana akan yadda abokan gaba Isra’ilawa suke ci gaba da hana shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza, wanda babban laifi ne da bai kamata a yi shiru a sa musu idanu ba.”

Haka nan kuma ya kara da cewa; Matakin da mu ka dauka na farko, amma idan har aka ci gaba, yunwa ta kara takurawa Falasdinawa, to matakin da za mu dauka zai fi na yanzu.”

Danagne da martanin da su ka kai wa jigin dakon jiragen yaki na Amurka a tekun “Red Sea”, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishar da yadda jiragen yakin na Amurka su ka kara yin nisa zuwa kilo mita 1300, domin tsoron hare-haren sojojin Yemen.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana cewa; Tun cin nasarar juyin musulunci, Iran ta zabi hanyar tattaunawa, saboda ta tabbatar da kyakkyawar niyyarta da kuma aiki da hankali a mu’amalrta da duniya.

Limamin na Tehran Ayatullah Saiddiki ya ce, a yayin tattaunawar da za a yi a tsakanin Iran da Amurka wacce za ta kasance ta hanyar shiga tsakani, Iran za ta ji abinda daya bangaren zai fada, sannan kuma ta bayar da jawabi, domin tabbatarwa da duniya cewa ita daula ce mai aiki da hankali, kuma ba ta tsoron tattaunawa.

Ayatullah Siddiki ya yi ishara da zancen jagoran juyin musulunci akan yadda bangaren da ake tattaunawar ba ya aiki da abubuwan da aka cimmawa da amincewa da su.

Haka nan kuma limamin na Tehran ya ambato jagoran juyin musuluncin na Iran yana bayyana yadda Amurka take kiyayya da Jamhuriyar da musulunci na Iran da addinin musulunci da kuma alkur’ani mai girma, saboda asarar manufofinta da ta yi a cikin Iran.

Ayatullah Siddiki ya kuma amabci cewa maganar da shugaban kasar Amurka yake yi na tattaunawa kai tsaye da Iran ba koma ba ne, sai yaudara da ba ta da tushe. Kuma saboda yadda Amurka ba ta aiki da duk wata yarjejeniya da aka cimmawa, don haka zama da ita gaba da gaba domin tattaunawa bai dace da mu ba.

Har ila yau, ya kuma ce, Shirin Iran na Nukiliya na zaman lafiya yana ci gaba da samun bunkasa saboda jagoranci na hikima na jagoran juyin juya halin musulunci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
  • Bam Ya Halaka Mutum 8, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Borno
  • Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • Iran da Amurka zasu ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa
  •  Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Yemen Ta Maida Martani Kan Wasu Cibiyoyin Ajiyar Makamai A Yaffa Don Tallafawa Gaza
  • Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%