Wata 11 da tuɓe rawanin wasu sarakuna a Sakkwato
Published: 18th, March 2025 GMT
An shiga wata 11 da Gwamnatin Jihar Sakkwato ƙarƙashin Gwamna Ahmad Aliyu ta tuɓe rawanin wasu sarakuna da take ganin sun yi abin da bai dace ba na shiga siyasa.
Tun bayan cire sarakunan, mutane sun yi tsammanin gwamnati za ta nada wadanda take muradi ne kai-tsaye domin su maye gurbin tubabbun sarakunan, amma shiru kamar ba wasu da ke jiran hukunci da sakayyar gwamnati mai ci.
Har yanzu gwamnati ba ta fito ta fadi dalilin rashin sake nada sababbin sarakunan ba domin ci gaba da wakilcin jama’a, ganin an bar garin kufai ba cikakken basarake.
A baya da ma sarukanan da aka tube sun jima suna dakon sakamakon bincikensu da gwamnatin ke yi, sai dai wasu jama’a musamman na ɓangaren jam’iyyar adawa na ganin bita da ƙulli ne gwamnatin ta yi musu.
Kakakin Gwamnatin Jihar Sakkwato, Abubakar Bawa ya ce, wadanda aka sauke daga mukamansu sun hada da iyayen kasar Unguwar Lalle da Yabo da Wamakko da Tulluwa da Illela da Dogon Daji, da Kebbe da Alkammu da Tambuwal da na Giyawa, a kananan hukumomi 10 na jihar.
Haka kuma an tube wasu iyayen kasa shida bisa dalilin cewa lokacin da aka nada su, an yi gaggawa ba a bi ka’ida ba.
Sai kuma wasu biyu da aka sauya wa wurin aiki, wadanda daya daga cikinsu ‘dan majalisar Sarkin Musulmi ne da sabon Magajin Gari da aka mayar masa sarautarsa ta da, yayin da za a ci gaba da gudanar da bincike a kan wasu iyayen kasar hudu.
Har ila yau, an amince da wasu iyayen ƙasa tara daga cikin wadanda aka bincika a kan su ci gaba da aikinsu.
To sai dai wasu jama’ar jiha musamman na ɓangaren jam’iyar adawa ta PDP na ganin wannan bai zo da mamaki ba domin da ma a cewarsu wannan gwamnatin ta ƙudiri aniyar cin zarafin sarakuna iyayen al’umma.
Hassan Sahabi Sanyinnawal kakakin jam’iyar ta adawa ce inda ya ce, rashin sanin aiki ne gwamnati ta ce, an naɗa wasu sarakuna ba bisa ka’ida ba.
Amma shi kuwa kakakin Gwamnatin Jihar Sakkwato kuma kakakin Jam’iyar APC mai mulki, Sambo Bello Danchadi ya ce, abin da gwamnati ta yi a kan ka’ida yake.
Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu a kan wannan lamarin, inda wasu suke ganin an yi daidai, duba da dalilan da aka bayar na tube sarakunan wasu kuma na ganin akasin haka, yayin da sauran iyayen kasa hudu da ake ci gaba da bincike a kansu ke dakon jiran sakamako.
An jima dai ana zargin sarakuna da tsoma hannu ga lamuran siyasa a Nijeriya, abin da kuma wasu lokuta yakan zo musu da mummunan sakamako.
Gaba dyaya gwamnati ta fita batun wannan lamari wanda ake ganin akwai buƙatar a tuna wa gwamnati domin lamari ne mai girma a wannan lokaci na matsalar tsaro, a ƙyale wasu jama’a ba cikakken sarki da ke kula da shige ficensu a yankinsu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno
Wani abin takaici ya sake afkuwa a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a Jihar Borno mai cike da tashin hankali, yayin da wani bam ya tarwatse a safiyar Asabar da rana, inda aƙalla mutane takwas ne suka mutu.
Wasu shaidun gani da ido na nuni da cewa fashewar bam ɗin da ake kyautata zaton mayaƙan Boko ne suka dasa shi ya tarwatsa wata motar bas ƙirar Toyota “Hummer Bus” da ke ɗauke da fasinjoji zuwa Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato An kama mutum 8 kan faɗan daba a KanoWata majiya mai tushe da aka zanta da ita, ta tabbatar da cewa aƙalla mutane bakwai da suka haɗa da direban motar ne ake fargabar sun mutu a wannan mummunan fashewar.
Titin Maiduguri zuwa Damboa ya kasance muhimmiyar hanyar mota da ta haɗa birnin Maiduguri zuwa ƙaramar hukumar Damboa da sauran al’ummomin kudancin Borno wadda a kullum ake fargabar bin ta lura da cewar tana gab da dajin Sambisa.
Don haka wannan lamari na baya-bayan nan ya zama babban abin tunatarwa game da barazanar tsaro da ke fuskantar matafiya da ke bin wannan hanya mai muhimmanci.
Har yanzu dai hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
To sai dai kuma babu shakka wannan harin zai ƙara dagula al’amura game da lafiyar masu tafiye-tafiye da sufuri a yankin da kuma yankin da ake da ’yan tada ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas.