Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujeru 54 na Hajj ga malamai da jami’an da za su jagoranci Alhazai don aikin Hajjin 2025.

Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga wakilin Radio Nigeria a Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujerun ne domin bai wa jami’ai  da malamai damar jagorantar Alhzan jihar a Najeriya da Saudiyya.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, wannan tsari da hukumar ta kirkiro shi ne irinsa na farko a tarihin Jihar Jigawa.

 

Ya bayyana cewa, an zabi jami’an da malamai maza da mata daga  daga kananan hukumomi 27 na jihar bisa cancanta.

Ya jaddada cewa, an zaɓi mutum biyu daga kowace karamar hukuma ta jihar.

Babban Daraktan ya bayyana cewa,  malamai da jami’an sun samu umarni don koyar da maniyyata game da wajiban Hajj, ka’idoji da kuma manyan ginshiƙan aikin Hajj domin su san yadda za su gudanar da ibadar Hajj yadda ya kamata.

 

Ya bayyana cewa, bayar da cikakken horo da ilimantar da maniyyata zai taimaka musu wajen gudanar da Hajj bisa koyarwar addinin Musulunci tare da wakiltar Najeriya da kyau.

Ya ƙara da cewa, za a ci gaba da gudanar da bita ga maniyyatan Hajj na 2025 a dukkan cibiyoyin da aka kebe bayan Ramadan.

Ahmed Labbo ya ce, hukumar za ta fara raba kayayyakin tafiya ga maniyyatan Hajj na 2025 nan ba da daɗewa ba.

A cewarsa, rarraba kayayyakin tafiya wadanda suka  haɗa da yunifom da jakunkuna zai fara nan gaba a hedkwatar hukumar da wasu cibiyoyi da aka ware a faɗin kananan hukumomi 27 na jihar.

Ya bayyana cewa, jirgin farko na jigilar maniyyatan jihar zai tashi a  watan Mayu 2025 kamar yadda Hukumar Hajj ta Kasa (NAHCON) ta tsara.

Labbo ya jaddada cewa, NAHCON ta ba Max Air damar jigilar maniyyatan jihar zuwa Saudiyya ta filin jirgin sama na Nuhu Muhammadu Sunusi International Airport.

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan ya gode wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kai da yake bai wa hukumar a kowane lokaci.

 

USMAN MUHAMMAD ZARIA 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Ya bayyana cewa ya bayyana cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago.

Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan.

Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba.

“Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun bar ma’aikatan kananan hukumomi da malaman firamare, amma mun ci gaba da hada kai da rokon su da su yi wa wadannan ma’aikata abun da ya kamata.

“Wasu daga cikinsu sun yi alkawari amma sun kasa cikawa. Muna fatan nan ba da jimawa ba za a warware wadannan damuwowin,” in ji shi.

Dangane da aiwatar da dokar cin kashin kan kananan hukumomi kuwa, shugaban NULGE ya yi bayanin cewa har zuwa yanzu Babban Bankin Nijeriya bai tuntubi kananan hukumomi kan bude asusun bankuna ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za A Samar Da Ababen Hawa Ga Malaman Sakandare A Jigawa
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto
  • UBEC Ta Bayyana Jihar Jigawa A Matsayin Abin Kuyi A Fannin Ilimi
  • Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi
  • Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje Sama Da 240 A Kebbi
  • ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja
  • Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe
  • Gwamnatin Sakkwato na biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 – NLC
  • UBEC Ta Yaba Wa Jigawa Kan Inganta Harkar Ilimi A Jihar