HKI Ta Nuna Damuwarta Da Jibge Sojojin Da Gwamnatin Masar Ta Yi A Yankin Sina
Published: 18th, March 2025 GMT
Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI.
Tun bayan da gwamnatin HKI ta gama lalata makaman gwamnatin kasar Siriya bayan ta taimaka ta kawo dan Daesh kan kujerar shugabancin kasar ta Siriya, kuma ta bayyana cewa yankunan da ta mamaye a kasar Siriya sun zama HKI ne har abada.
Banda haka mun ga yadda sabon shugaban kasar ta Siriya Julani ya yi shiri da bakinsa a kan mamayar da HKI takewa kasar Siriya da kuma yadda ta kai hare-hare fiye da dubu guda kan kasar tana lalata makamanta, ko wa ya fahinci cewa, siriya ta gama yawo,. Kuma ba zata taba daga ko tsinke a gaban HKI ba.
Tashar talabijin ta Presstv ba ce, a halin yanzu hankalin yahudawa ya koma kan kasar Masar, wacce take ganin bangare na HKI kuma kasar tana iya zama matsala gareta, duk tare da nasarorin da ta samu ya zuwa yanzu na mamayar kasashen larabawa.
Tsohon babban haffsan sojojin HKI Herzi Halevi ya fito fili ya na cewa suna cikin damuwa dangane da kasar Masar. Don ta sami ci gaba sosai a bangaren mallakan makamai na zamani.
Ya kuma kara da cewa, a shekara ta 2011 da aka yi juyin juya halin na yanuwa musulmi, wato Muhammad Mursi sun ji tsaro, amma sun dan numfasa bayan an kauda Mursi. Sai dai a halin yanza akwai barazana na kara karfi a bangaren kasar ta Masar, musamman bayan yakin 7 ga watan Octoba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Masar
এছাড়াও পড়ুন:
Za a mayar da tubabbun ’Yan Boko Haram cikin al’umma – Gwamna Buni
Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC).
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar rundunar OPSC ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa.
Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwajiGwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta tuntuɓar juna da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jihar.
Ya koka da yadda rikicin da aka kwashe sama da shekaru 15 ana yi ya laƙume rayukan dubban mutane a Yobe, da lalata dukiyoyin jama’a da na masu zaman kansu tare da raba magidanta da dama da garuruwansu na asali.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta gane cewa, ba dukkan ’yan ƙungiyar ta’addancin ne ke shiga cikin kisan kai ba, yana mai cewa tsarin kishin ƙasa ya ba da damar ceto da kuma mayar da waɗanda suka nuna nadama ya zuwa ga al’ummominsu.
“Mun yi imanin cewa, an tura wasu mutane shiga cikin ’yan ta’adda ta hanyar ƙarfi ko koyarwar aƙida.”
“Tare da ci gaba da ƙoƙarinsu, za su iya tuba, gyarawa da komawa rayuwa ta yau da kullun a matsayin ‘yan ƙasa da ke da ‘yanci.” In ji Buni.
Gwamnan ya ce tubabbun ‘yan Boko Haram 390 da suka haɗa da ‘yan asalin Jihar Yobe 54 ne za su kammala karatu tsakanin ranakun 14 zuwa 19 ga Afrilu.
Ya ce, jihar ta samar da wasu tsare-tsare ta hanyar ma’aikatar Jinƙai da kula da bala’o’i domin tabbatar da sake dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata.