Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja
Published: 18th, March 2025 GMT
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen kula da filaye na Abuja, Chijioke Nwankwoeze.
Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na shekara shekara.
Wasiƙar ta ce PDP ta gaza biyan kuɗin tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2006 zuwa 1 ga watan Janairun 2025, duk da sanarwar da hukumar gudanarwar babban birni (FCTA) ta wallafa a jaridu da dama tun daga shekarar 2023 kan buƙatar biyan kuɗaɗen.
Aminiya ta ruwaito cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da Ministan ya ƙwace a Abuja.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Noma Na Gambiya: Hadin Kan Gambiya Da Sin A Fannin Aikin Gona Ya Haifar Da Sakamako Mai Kyau
Ministan noma na kasar Gambiya Demba Sabally ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya cewa, goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona na Gambiya a shekarun baya-bayan nan.
Ministan ya ce, yawan amfanin gona da kasar ta Gambiya ke samu na ci gaba da karuwa, inda yawan shinkafar da kasar ta samar ya haura tan 48,000 a shekarar 2024, wanda ya kafa tarihi. Sabally ya kuma bayyana cewa, kirkire-kirkire a fannin samar da ababen more rayuwa, da fasahohin aikin gona masu yawan gaske da tawagogin kasar Sin suka yi amfani da su, sun taka rawa wajen kai wa ga wannan matsayi.
Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (3) Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan MajalisuYana mai cewa, tawagar kwararrun kasar Sin sun ba da taimako a kasar Gambiya ta hanyar gabatar da nau’o’in shinkafa masu inganci da suka hada da ire-iren da aka tagwaita da masu samar da girbi mai yawa, wadanda ke da matukar muhimmanci ga bunkasa aikin gonar Gambiya.
Sabally ya kammala da cewa, Gambiya za ta ci gaba da tura ma’aikatan aikin gona zuwa kasar Sin don samun horo mai zurfi, kuma yana fatan zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasarsa da Sin a fannin aikin gona, da sabbin fasahohi, da bunkasa hazaka. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp