Kasar Sin na matukar adawa da haramta amfani da kirkirarriyar basira ta DeepSeek da gwamnatin Amurka ta yi a ranar Talata, biyo bayan rahoton da kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar na cewa, ma’aikatar cinikayya ta Amurka ta haramtawa ma’aikata amfani da DeepSeek kan na’urorin da gwamnati ta samar musu.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana adawa da zuzuta batun tsaron kasa fiye da kima, da siyasantar da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, cinikayya da fasaha. Mao ta kara da cewa, kasar Sin za ta kare hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Putin Na Kasar Rasha Zai Zanta Ta Wayar Tarho Da Tokwaransa Na Kasar Amurka Donal Trump

A yau Talata ce ake saran shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Amurka Donal Trump, kuma wannan shine zantawar shuwagabannin kasashen biyu tun shekaru masu yawa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto kakakin Fadar Krimlin Dmitry Peskov yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa a halin yanzu ana shirye-shiryen zantawar shuwagabnnin biyu.

Peskov ya kara da cewa tattaunawar tasu zai maida hankali ne kan yakin Ukraine da matsalolin da suke kewaye da yakin.

Yau ita ce ranar da kasar Rasha ta hade yankin Cremear ga kasar Rasha, a shekara ta 2014. Kwace yankin dai ya jawo matsaloli da dama tsakanin Amurka da Rasha a lokacin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas 
  • Harin Jirgin Yakin Sojoji Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 18 A Kasuwa
  • Shugaban Putin Na Kasar Rasha Zai Zanta Ta Wayar Tarho Da Tokwaransa Na Kasar Amurka Donal Trump
  • HKI Ta Nuna Damuwarta Da Jibge Sojojin Da Gwamnatin Masar Ta Yi A Yankin Sina
  • Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da Faransanci
  • Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da da Faransanci
  • Baka’i: Za Mu Mayar Da Martani Akan Wasikar Trump Bayan Yin Nazari
  • Yemen: Amurka Ta Sake Kai Wani Harin A Kasar Yemen
  • Tsohuwar ɗaliba ta kai ƙarar makarantar da ta kammala