Aminiya:
2025-03-18@20:20:35 GMT

Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka

Published: 18th, March 2025 GMT

Ƙungiyar Hamas ta ɗora alhakin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar yau Talata a Zirin Gaza kan Amurka.

A wata sabuwar sanarwa da Hamas ta fitar, ta ce Amurka ce ke da “alhakin kisan gillar” da aka yi a Gaza bayan da ta bayyana cewa Isra’ila ta shaida wa Amurka shirinta na kai hare-haren gabanin kai harin.

Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza

Sanarwar ta ce hakan ya “tona asirin ƙaryar da suke yi na iƙirarinsu kan damuwa da kawo ƙarshen yaƙin.

“Muna buƙatar ƙasashen duniya su ɗauki matakin gaggawa na kama masu aikata laifukan yaƙi da masu goya musu baya,” in ji Hamas.

A gefe guda kuma kafar yaɗa labarai da ke da alaƙa da Hamas, mai suna Filastin, ta ce an kashe jami’an gwamnatin Hamas huɗu a hare-haren Isra’ila.

Hazalika, shugaban hukumar lafiya da Hamas ke jagoranta, Munir al-Barsh ya ce mutane fiye da 660 aka jikkata a hare-haren, kuma wasu da dama na ƙarƙashin ɓaraguzai.

Majiyoyin kiwon lafiyar Gaza sun shaida wa gidan Talabijin na Al Jazeera cewa fiye da mutane 400 ne aka kashe, kuma mafi yawancinsu mata da ƙananan yara da kuma dattawa.

Harin wanda ke nuna kawo ƙarshen yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ƙulla tsakanin Isra’ila da Hamas a watan Janairu, Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da shi ne bayan da Hamas ta ƙi sako ragowar mutanen da ta yi garkuwa da su.

Wani jami’in Isra’ila ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, za su ci gaba ta kai hare-hare har sai sun kawar da shugabannin Hamas da gine-ginensu da kuma kayan aikinsu.

Fadar White House ta bakin sakatariyar yaɗa labaranta Karoline Leavitt, ta ce sai da Isra’ila ta sanar da ita, kafin ɗaukar matakin kai harin.

“Isra’ila ta sanar da gwamnatin Trump da fadar White House kan harin da suka kai Gaza a daren yau, kamar yadda shugaba Trump ya bayyana Hamas da Houthis da kuma Iran, da ke neman addabar Isra’ila har ma da Amurka, za su ɗanɗana kuɗarsu.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Falasɗinawa Isra ila Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyoyin Falasdinawa Suna  Cigaba Da Yin Allawadai Da Hare-haren Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta  Hamas ta yi Allawadai da Hare-haren Amurka da Birtaniya akan kasar Yemen

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani na yin tir da hare-haren da jiragen yakin Amurka da Birtaniya su ka kai wa Birnin San’aa a jiya Asabar da dare.

Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da bayani na yin Allawadai da Amurka saboda harin da ta kai wa Yemen din, tana mai bayyana abinda ta aikata da cewa abin kunya ne da nuna goyon bayan ga laifukan da HKI take aikatawa akan al’ummar wannan yankin.

Kungiyar Jiahdul-Islami ta kuma yi jinjina ga kasar Yemen saboda yadda su ka tabbatar da jarunta ta asali irin ta Larabawa da musulmi wajen nuna goyon bayan mutanen Gaza da al’ummar Falasdinu.

Kwamitin al’umma na goyon bayan gwgawarmayar al’ummar Falasdinu ya bayyana harin na Amurka da Birtaniya akan Yemen da cewa, nuna goyon bayan ne karara ga HKI.

Bayanin ya kuma ce; Maharan ba za su karya kashin bayan al’ummar Yemen  ba da suke tsayin daka wajen taya Falasdinawa fada da kalubalantar killace mutanen Gaza da HKI ta yi, bisa goyon bayan Amurka.

Ita kuma kungiyar “Harkatul-Mujahidin” ta yi kira ne ga  rayayyun al’ummu da ‘yan gwgawarmaya da su hada karfi da karfe domin  fuskantar wuce gona da irin ‘yan sahayoniya da Amurka, tare da kara da cewa; Babu abinda zai takawa  masu daga hancin  da girman kai, birki,sai karfi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 330 Sun Mutu Yayin da Isra’ila Ta Kai Wa Gaza Sabbin Hare-hare 
  • Gaza: Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sanadiyar Hare-Haren HKI Ya Dara 400
  • Sayyid Husi: Idan Amurka Ta Ci Gaba Da Kai Mana Hare-hare To Muna Da Hanyoyin Gasa Mata Aya A Hannu
  • Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza
  • Yemen: Amurka Ta Sake Kai Wani Harin A Kasar Yemen
  • Adadin Shahidan Falasdinawa A Gaza Ya Karu Da 14 A Jiya Lahadi Saboda Hare-Haren Sojojin HKI
  • Hizbullah ta yi Allah wadai da harin Amurka da Birtaniya a kan Yemen
  • Fiye Da Mutane 20 Ne Su Ka Yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren  Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen
  • Kungiyoyin Falasdinawa Suna  Cigaba Da Yin Allawadai Da Hare-haren Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen