An Ware Sama Da Naira Biliyan 1.5 Don Fara Aiki A Sabon Kamfanin Injinan Noma Na Jigawa
Published: 18th, March 2025 GMT
A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, an kafa kamfanin ne domin rage tsadar sarrafa kayayyakin amfanin gona a fadin jihar.
Ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da naira miliyan dari tara da sittin da tara domin ci gaba da aiwatar da ayyukan kamfanin injinan noma.
Ya ce, wannan amincewa ta hada da biyan harajin kwastam da kudaden haraji na gwamnati kan kayan aikin injinan noma da kuma sassan gyara da aka sayo daga kasar Sin.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewa, majalisar ta tattauna kan wani kudirin doka da ya shafi kafa Asusun Tallafin Ibtila’in Ambaliyar ruwa na Jihar Jigawa.
Kwamishinan ya kara da cewa, amincewar ta yi daidai da kudirin Gwamna Umar Namadi na kawo dauwamammen mafita kan matsalolin ambaliya a jihar.
Ya ce, bayan tattaunawa, majalisar ta amince da kudirin dokar tare da mika shi zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Kallo Daya Mutum Za Yi Min Ya Gane Masana’antar Kannywood Ta Canza Rayuwata -Farida Abdullahi
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar wadanda ta ke tunanin za su tsaneta kasancewarta jarumar fim sun zamo masoyanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp