Aminiya:
2025-03-18@22:24:01 GMT

Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau

Published: 18th, March 2025 GMT

Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau.

Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja.

Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji

Wakilinmu ya ruwaito cewa a yanzu ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada ne zai gaje shi a wannan kujera
ta hakimanci.

Farfesa Ango Abdullahi yana ɗaya daga cikin mazan jiya da suka yi ragowa a Nijeriya.

Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ɗaya ne daga cikin dattawan da al’umma suke buƙata musamman a wannan zamani.

Yana ɗaya daga cikin masu bayyana ra’ayin su a kowanne irin yanayi don jawo hankalin shugabanni da al’ummomi da nufin kyautata rayuwa.

Kazalika, Farfesa Ango Abdullahi shi ne na biyar a tarihin cikin jerin waɗanda suka riƙe muƙamin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tuni dai Masarautar Zazzau ta bayyana Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada wadda ƙani ne ga shi Farfesa Dahiru Ango Abdullahi a matsayin sabon Magajin Rafin Zazzau.

Sai dai masarautar ta ce zuwa nan gaba kaɗan za ta fidda ranar da za a yi bikin naɗin sabon Magajin Rafin Zazzau.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawan Arewa Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Magajin Rafin Zazzau Abdullahi ya

এছাড়াও পড়ুন:

Fizishkiyan:  Addinin Musulunci Da Kur’ani Mai Girma Suna Tabbatar Da Shimfida Adalci

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Dukkanin batutuwan  da Musulunci da kuma al’kur’ani maigirma suke bijiro da su, sun ginu ne akan ginshikin gaskiya da kuma adalci.

Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Idan har wadannan ginshikan biyu su ka zama ana aiki da su a cikin al’umma, to za a sami shiriya.

Shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce; A wannan lokacin muna da bukatuwa da koyar da dalibai da ‘ya’yanmu domin su kai ga mataki na koli na ilimi da kuma kyawawan halaye, ta yadda za su zama karfin madogara da hikima da kyawawan halaye a cikin al’umma.

Shugaban na kasar Iran ya kuma ce: Abubuwan da musulunci da kuma al’kur’ani suke bijiro da su, sun ginu ne akan ginshikai biyu da su ne  gaskiya da kuma adalci a cikin dukkanin fagage.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fizishkiyan:  Addinin Musulunci Da Kur’ani Mai Girma Suna Tabbatar Da Shimfida Adalci
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [10]
  • Ba A Taɓa Shugaban Ƙasar Da Ya Kai Mahaifina A Nijeriya Ba – Ɗan Shugaba Tinubu
  • Ba A Taɓa Shugaban Ƙasar Da Ya Kai Mahaifina A Nijeriya Ba – Ɗan Shugaban Tinubu
  • Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A Legas  Ya Koma APC Daga PDP
  • Shugaban Kasar Amurka Ya Kara Yawan Kasashen Da Ya Sa Wa Takunkumin Shiga Amurka
  • Cikar FRCN Kaduna Shekaru 63: An Bukaci Gwamnonin Arewa Su Tabbatar Da Dorewar Gidan Rediyon
  • Cikar FRCN Shekaru 63: An Bukaci Gwamnonin Jihohin Arewa Su Tabbatar Da Dorewar Gidan Rediyon
  • Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi