Aminiya:
2025-04-21@02:09:11 GMT

An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas

Published: 19th, March 2025 GMT

Mazauna sun shiga zaman ɗar-ɗar a yayin da motocin yaƙi na sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Ribas.

Wannan dai na zuwa ne jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Jihar Ribas

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa fiye da motocin soji 10 aka hanga suna sintiri a kan hanyar zuwa gidan gwamnatin yayin da wasu motocin yaƙi masu sulke suka tsaya wuri-wuri a hanyar.

Majiyar ta ce titunan birnin na Fatakwal sun zama fayau a yayin da mazauna suka tsere gidajensu.

Babu tabbaci ko gwamnan da aka dakatar, Similanayi Fubara yana cikin gidan gwamnatin a halin yanzu.

Sai dai majiyoyi sun ce akwai yiwuwar gwamnan ya samu labarin cewa za a ayyana dokar ta ɓacin tun kafin faruwar lamarin.

Bayanai sun ce gwamnan ya shafe tsawon wunin wannan rana ta Talata yana ganawa da ’yan majalisar zartarwarsa.

A halin yanzu dai birnin na Fatakwal ya zama fayau a yayin mazauna da ’yan kasuwa duk sun koma gidajensu.

Dalilin da Tinubu ya ayyana dokar ta ɓacin

Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.

Tinubu ya sanar da matakin ne a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar da yammacin ranar Talata.

A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.

“Jihar ta tsaya cik tun bayan ɓarkewar rikicin siyasar inda aka tauye wa al’ummar jihar hakkinsu na cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.

“Na yi iyakar bakin ƙoƙarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin.

“Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na yi amfani da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

“A kan haka, na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025.

“Da wannan bayani, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Mrs Ngozi Odu da kuma dukkanin zaɓaɓbun ƴanmajalisar dokokin Jihar Ribas, an dakatar da su na wata shida, a matakin farko.

“A halin yanzu, na naɗa Vice Admiral Ibokette Ibas a matsayin wanda zai gudanar da lamurran jihar, domin amfanin al’ummar jihar,” in ji Tinubu.

Sai dai a cikin jawabin nasa, Tinubu ya bayyana cewa wannan doka da ya ƙaƙaba ba ta shafi ɓangaren shari’a na jihar ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Jihar Ribas Siminalayi Fubara a ayyana dokar ta

এছাড়াও পড়ুন:

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayyana Cewa: Makiya Suna Adawa Da Fadada Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna adawa da fadada dangantakar Iran da Saudiyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman a jiya Alhamis.

A yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, alakar da ke tsakanin Iran da Saudiyya za ta kasance mai amfani ga kasashen biyu, kuma kasashen biyu za su iya taimakawa juna.

Imam Khamenei ya yi nuni da cewa, akwai makiya da suke adawa da fadada alaka a tsakanin kasashenmu biyu, kuma wajibi ne a shawo kan wadannan munanan manufofin, kuma a shirye Iran take ta yi hakan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da ci gaba da Iran take samu a fagage daban-daban yana mai cewa: A shirye take ta taimaka wa Saudiyya a wadannan fagage.

Jagoran ya jaddada wa Ministan Tsaron Saudiyya cewa: Yana da kyau ’yan’uwanmu da ke yankin su hada kai da taimakon juna maimakon dogaro da wasu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fursunoni 9 Sun Tsere Daga Gidan Gyara Hali A Jihar Kwara, An Cafko Guda Daya
  • Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue
  • Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
  • Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu?
  • Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi
  • Dalilan Da Suke Sa Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Ci Gaba Da Tafka Asara A Halin Yanzu
  • Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
  • Dokar-ta-baci: Shugaban Majalisar Wakilai Ya Gargadi Kantoman Ribas
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayyana Cewa: Makiya Suna Adawa Da Fadada Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya
  • Tinubu Ya Tsawaita Zaman Sa A Faransa