Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Sanar Da Shahadar Abu Hamza Kakakin Dakarunta Na Sarayal-Kudus”
Published: 19th, March 2025 GMT
A jiya Talata ne dai kungiyar ta Jihadul-Islami ta kaddamarwa da al’ummar Musulmi shahadar Naji Abu Saif, wanda ake yi wa lakbi da Abu Hamza, da ya kasance kakakin dakarun “Sarayal-Kudus” bayan da ‘yan sahayoniya su ka yi masa kisan gilla tare da iyalansa da iyalan dan’uwansa.
A bayanin da ta fitar, kungiyar ta Jihadul-Islami ta ce; Duniya ta yi sanayya da sautin shahidin wanda ya kasance sauti ne na gwagwarmaya da ba ya tsoron wani zargi akan tafarkin Allah, wanda kuma Allah ya yi wa baiwar fasahar zance da kuma jarunta da kare hakkokin al’ummarmu ta Falasdinu.
Kungiyar ta kuma ci gaba da cewa,kisan gillar da ‘yan sahayoniyar su ka yi wa Abu Hamza wani sashe ne na jerin kisan kiyashin da suke yi wa al’ummar Falasdinu wanda ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama, kananan yara maza da mata.
Kungiyar ta Jiahdul-Islami ta kuma ce;Amurka ce take karfafawa ‘yan sahayoniya gwiwa da kuma taimaka musu akan laifukan da suke yi, tare da bayyana mamaki akan yadda duniya ta sanya idanu tana kallo.
Sai dai kungiyar ta ce; Abinda yake faruwa babu abinda zai karawa Falasdinawa sai tsayin daka da jajurcewa wajen kare hakkokinsu da dakile manufofin abokan gaba baki daya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
Jami’an tsaro Gwamnatin Tarayya suna sassauta wa masu kashe mutane babu gaira babu dalili a Jihar Filato, a cewar tsohon jihar na mulkin soji, Rear Admiral Samuel Bitrus Atukum.
Da yake tsokaci kan kisan gillar da ka yi wa mutane 52 tare da lalata kadarori na miliyoyin naira baya-bayan nan a yankin Ƙaramar Hukumar Bokkos, Atukum ya ce, “Ina da matsala kan yadda jami’an tsaro ke tunkarar matsalar. A gani na suna sassauta musu. Mene ne abu mai wahala a ba wa sojoji umarni su je maɓoyar masu wannan aika-aika su kamo su?
“Daga kan tsaunuka mutanen nan suke saukowa ɗauke da makamai su halaka jama’a, sannan su ɓace, kuma a nan suke ɓoye makamansu. Saboda haka ya kamata jami’an tsaro su yi fiye da abin da suke yi yanzu.
“Kamata ya yi a ayyana waɗannan mutane a matsayin ’yan ta’adda, saboda ta’addanci suke yi, amma an kasa, sai a je ana kama masu ƙananan laifi da sunan manyan laifuka,” in ji Atukum wanda shi ne gwamnan Filato daga 1984 zuwa 1985.
Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Mutane 300 sun kamu da cutar sanƙarau SakkwatoYa bayyana cewa a lokacin da yake gwamna rikicin addini na ƙungiyar Maitatsine ya ɓarke, amma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci aka murƙushe shi, saboda gwamnati ta tari matsalar tun daga tushe kafin a je ko’ina.
Ya ce idan za a ɗauki irin matakin daga sama a kan matsalar tsaron Filato, shugaban ƙasa ya ba wa jami’an tsaro umarni a matsayinsa na Babban Kwamandan Tsaron Ƙasa, za su yi abin da ya kamata.
“Amma ba a ba da umarni ko ɗaukar mataki ba, sai mutane sun yi ta ƙorafi kan matakin da gwamnati ta ɗauka, sai a fito ana cewa za a kamo waɗanda suka aikata abin, a hukunta su daidai da abin da doka ta tanada. Wannan shi ne abin da muke ta ji.”
Ya ce, “Da ni ke da iko, da umarni da wa’adi ƙarara zan na wa jami’an tsaro cewa ga abin da nake so. Idan shugaban ƙasa da gaske yake kan matsalar tsaro, umarni kawai zai bayar kuma yana da tasiri a kan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, duk abin da yake so za ta yi aiki a kai, kuma a tafi tare da ɗaukacin al’ummar ƙasa.
“Amma ya za a yi ka ce kana maganin abun, amma ba a ga alamar komai ba? Wa zai ɗauka da gaske kake, alhali ba a ga an kamo masu aikata laifin an hukunta su ba?
“A wannan yanayi da matsala ke fama da matsalar rashin aiki, mutane za su yi ta amfani da irin wannan giɓi wajen yin irin waɗannan aika-aika da muke gani.
“Har ta kai ga masu yin wannan ta’asa na ba da umarnin cewa ga wanda suke so a naɗa a matsayin shugaɓan wata hukumar tsaro, ko kuma a sauke wanda yake kai,” in ji tsohon gwamnan sojin.