Sojojin Kasar Yemen Sun Kai Wa HKI Hari Da Makami Mai Linzami
Published: 19th, March 2025 GMT
A ci gaba da taya Falasdinawa fada da sojojin Yemen suke yi, sun kai wa sansanin jiragen sama na HKI dake saharar “Nakab” hari da makami mai linzami samfurin “Ballistic’ wanda ya fi sauti sauri.
A wata sanarwa da sojojin Yemen su ka yi da marecen jiya Talata sun bayyana cewa; a karkashin taimakawa Falasdinawa da ake zalunta, da kuma mayar da martani akan kisan kiyashin da abokan gaba ‘yan sahayoniya suke yi wa ‘yan’uwanmu a Gaza, sojojin Yemen sun kai hari da yardar Allah akan sansanin sojan sama na Nivatim” da makami mai linzami wanda ya fi sauti sauri, mai suna “Falasdinu 2” sun bisa yardar Allah ya isa inda aka harba shi.
Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa; Sojojin Yemen za su fadada hare-haren da suke kai wa a cikin Falasdinu dake karkashin mamaya a cikin sa’o’i da kuma kwanaki masu zuwa, matukar abokan gaba ba su daina kai wa Gaza hare-hare ba.”
Kakakin sojan Yemen janar Yahya Sari ya kuma bayyana cewa; al’ummar Yemen da ta kunshi jagorori, al’umma da kuma soja, ba za su zama ‘yan kallo ba ana yi wa ‘yan’uwanmu kisan kiyashi a Gaza.” Har ila yau janar Sari ya ce; “ Bisa yardar Allah sojojin na Yemen za su yi amfani da dukkanin makaman da take da su domin kare da taimakon Falasdinawa da ake zalunta.”
Janar Sari ya kuma ce; Ba za su daina kai hare-haren ba, har zuwa lokacin da za a dakatar da killace Gaza da ci gaba da kai musu kayan agaji a suke da bukatuwa da su, kuma za su ci gaba da hana jiragen ruwa wucewa zuwa HKI.
A gefe daya, sojojin na Yemen sun sanar da sake kai hari akan jirgin dakon jiragen yaki na Amurka dake cikin tekun “Red Sea” wanda shi ne karo na 4 a cikin sa’o’i 72.
Janar Sari ya kuma sanar da cewa sun yi nasarar dakile wani hari da ake gab da kai wa Yemen ta sama,kuma hare-haren na Amurka ba za su hana su ci gaba da hana su aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu ba na addini da ‘yan’adamta dangane da al’ummar Falasdinu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 45 Sun Rasa Rayukansu A Wani Sabon Hari A Filato
Sai dai har yanzu rundunar ‘yansandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ƙoƙarin da samun martaninsu ya ci tura.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Filato ta nuna damuwa kan hare-haren da ake samu a wasu sassan faɗin jihar, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa a zuƙatan jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp