Leadership News Hausa:
2025-04-13@09:49:43 GMT

WSCIJ Ta Naɗa Farfesa Umaru Pate A Kwamitin Amintattu

Published: 19th, March 2025 GMT

WSCIJ Ta Naɗa Farfesa Umaru Pate A Kwamitin Amintattu

Da wannan sabon matsayi, Farfesa Pate, zai haɗa kai da sauran ƙwararru da ke aiki domin tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da inganta shigar da al’umma cikin harkokin shugabanci, wanda ake kyautata zaton ƙwarewarsa za ta taimaka wajen tsara sabbin hanyoyi da cibiyar WSCIJ za ta amfana.

 

WSCIJ, wacce an sanya mata suna daga fitaccen marubuci kuma masanin adabi, Farfesa Wole Soyinka, cibiya ce mai zaman kanta da ke amfani da binciken ƙwaƙwaf a aikin jarida domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da inganta tsarin shugabanci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gobara Ta Ƙone Shaguna 12 A Kasuwar Siminti Ta Oyo

A ƙalla shaguna 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi da daddare a Agodi Gate, birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a ginin Block A  na kasuwar Siminti ta Mayegun, Araromi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar.

Shugaban hukumar, Akinyemi Akinyinka, ya bayyana cewa jami’ansu sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:02 na dare, inda nan take suka tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Cfs Jimoh. Bayan isarsu, sun tarar da shaguna da dama na ci da wuta, amma cikin gaggawa suka dakile yaɗuwar gobarar zuwa sauran shagunan da ke kusa.

Gobara Ta Kashe Yaro A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Maiduguri Gobara Ta Ƙone Sabon Ginin Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Mata Na Jami’ar Sokoto 

Akinyinka ya bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wutar lantarki mai ƙarfi. Ya ƙara da cewa an kare dukiyoyi da darajarsu ta kai biliyoyin Naira a kasuwar, duk da cewa shaguna 12  sun ƙone baki ɗaya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsohon Kocin Super Eagles, Christian Chukwu, Ya Rasu Yana Da Shekaru 74
  • Za A Samar Da Ababen Hawa Ga Malaman Sakandare A Jigawa
  • Har Yanzu Shugabanci NNPP Na Hannunmu – Tsagin Kwankwaso
  • Masarautar Kauru Ta Bayyana Rashin Sha’awarta Kan Shiga Sabuwar Jihar Gurara
  • Tawagogin gwamnatin Kongo da kungiyar M23 sun isa  Doha domin tattaunawa
  • Gobara Ta Ƙone Shaguna 12 A Kasuwar Siminti Ta Oyo
  • UBEC Ta Yaba Wa Jigawa Kan Inganta Harkar Ilimi A Jihar
  • Huawei Ya Daddale Yarjejeniya Da Kenya Don Habaka Kwarewar Ma’aikatan Kasar A Fannin Dijital
  • Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur 
  • Ku Kyautata Rayuwar Jama’a Ba Taku Ba — Buhari Ga Gwamnonin APC