Aminiya:
2025-04-13@11:06:08 GMT

Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

Published: 19th, March 2025 GMT

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda.

Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi

Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar.

‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’

Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya kasance yana aiki ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce duk da tankiyar siyasa, ya ci gaba da gudanar da aiki don tabbatar da tsaro da inganta rayuwar mutanen Jihar Ribas.

Ya ƙara da cewa bayan shugaban ƙasa ya shiga tsakani domin kawo zaman lafiya, ya kiyaye duk yarjejeniyar da aka cimma, ciki har da karɓar kwamishinonin da suka yi murabus a baya.

Bayan haka, gwamnan ya ce ya amince da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke domin mayar da jihar kan turbar da doka da oda suka tanadar.

‘Majalisar dokokin Ribas ta hana ruwa gudu’

Gwamnan ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatinsa ta yi domin samar da zaman lafiya, ’yan majalisar dokokin jihar sun kawo cikas.

Ya ce yana aiki ne don tabbatar da an kare dimokuraɗiyya da ci gaban mutanen jihar amma majalisar ta riƙa hana ruwa gudu.

A cewarsa, duk da saɓanin siyasa da ake fama da shi, gwamnatinsa na biyan albashin ma’aikata tare da aiwatar da manyan ayyuka don ci gaban jihar.

Fubara ya bayyana cewa duk da ƙalubalen siyasar, ya tabbatar da jihar na cikin kwanciyar hankali kuma babu wata barazanar tsaro da ake fuskanta.

A ƙarshe Fubara ya buƙaci mutanen jihar da su zauna lafiya tare da guje wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace don kare dimokuraɗiyya da tabbatar da ci gaban jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Ribas Siminalayi Fubara tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Za A Samar Da Ababen Hawa Ga Malaman Sakandare A Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta samar da ababen hawa ga shugabannin makarantun babbar  sakandare a fadin jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin makarantu a garin Dutse.

A cewarsa, za a gyara gidajen ma’aikatan makarantun sakandare domin saukaka matsalar masauki ga malamai da sauran ma’aikata da ba malamai ba.

Farfesa Chamo, wanda Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Ilimi, Malam Abdullahi Hudu, ya wakilta, ya ce taron ya na da nufin tattauna shirin dawowa  makarantu bayan hutun da aka yi a jihar.

Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta sanya bangaren ilimi a sahun gaba saboda muhimmancinsa ga ci gaban jihar.

Kwamishinan ya nuna cewa gwamnatin jihar ta dauki malamai 7,000 domin inganta tsarin koyarwa a makarantu, inda ya kara da cewa za a dauki ma’aikatan girki na J-Cook domin kara karfafa harkar gudanarwar makarantu.

A jawabansu daban-daban, wasu daga cikin Daraktoci da Shugabannin makarantu, sun bukaci a sake duba kudaden gudanar da makarantu, da samar da kwamfutoci da kayan aikinsu, da bayar da tallafi da kuma samar da malamai domin inganta ayyukan koyarwa.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sama da mutane 1,560 ne sukayi shahada tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki Gaza
  • Za A Samar Da Ababen Hawa Ga Malaman Sakandare A Jigawa
  • Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi
  • Hanyoyi Biyar Na Kare Kajin Gidan Gona Daga Tsananin Zafi
  • Hisbah Ta Lalata Katan 51 Na Giya a Jihar Yobe
  • Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto
  • An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya
  • An Kafa Dokar Kai Da Komowa A Kudancin Kasar Syria
  • ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja
  • Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta