Za Mu Bi Doka Domin Dawo Da Haƙƙinmu – Fubara
Published: 19th, March 2025 GMT
Fubara ya ƙara da cewa, duk da rikicin siyasar da ake fama da shi, gwamnatinsa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma ana biyan ma’aikata albashinsu tare da ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar.
Ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa dimokraɗiyya ta ci gaba da ƙarfafa a jihar.
An fara samun matsala a siyasar Jihar Ribas tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin Fubara da tsohon gwamnan jihar, wanda yanzu shi ne Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Rikicin ya kai ga cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka yi barazanar tsige Fubara daga muƙaminsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yan Majalisa Dokar Ta ɓaci Fubara Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Nijeriya Sun Nuna Damuwarsu Kan Kashe-kashen Mutane A Filato
Sun roƙi a dakatar da duk wani nau’in tashin hankali da ake yi a jihar.
Ƙungiyar ta kuma yi addu’arsamun rahamar Allah ga waɗanda suka rasa rayukansu tare da fatan samun sauki ga waɗanda suka jikkata.
Ta kuma yi kira ga kowa da kowa da ya rungumi zaman lafiya da tattaunawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp