MAfi yawancin mambobin kwamitin tsaron sun yi tir da harin da sojojin HKI su ka kai wa mutanen Gaza a cikin daren shekaran jiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar fiye da Falasdinawa 400.

 Wakilin kasar Rasha a MDD  ya bayyana cewa; Sake bude yaki a Gaza, yana nufin korar Falasdinawa daga kasarsu” ya kuma jaddada cewa; “  Wajibi ne ga kwamitin tsaro ya yi duk abinda zai iya yi, domin sake tsayar da wutar yaki, bai kuma kamata a ce an sake maimaita kurakuren baya ba.

Shi kuwa wakilin kasar Aljeriya a MDD, ya bayyana ya zargi HKI da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, yana mai jaddada cewa; Wannan lokaci ne da hukunta masu laifi, domin babu wanda ya fi karfin doka.” Haka nan kuma ya ce;  Yanzu duniya  ta daina kawar da kanta daga laifukan da ‘yan mamaya suke yi.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

IRGC: Iran ba za ta fara yaki ba amma za ta mayar da martani ga duk wata barazana

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma  a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya.

Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi, bayan da Washington ta zargi Tehran da taimakawa sojojin Yaman a hare-haren da suka rika kaiwa haramtacciyar kasar Isra’ila a baya-bayan nan tare da yin kira da ta daina yin wanann zargi maras tushe balantana makama.

Salami ya ce, “Iran ba za ta taba zama mai fara yaki ba, amma idan aka fuskanci barazana, za ta mayar da martani mai tsanani.”

Shugaban kasar Amurka ya sake alakanta ayyukan da kungiyar Ansarullah ta Yaman ga Iran, ya kuma ce dole ne Iran ta daina  goyon bayan kungiyar mai gwagwarmaya.”

Salami ya jaddada cewa, mutanen Yemen al’umma ce mai ‘yanci da ke bin manufofi na kashin kansu ba tare da an yi musu katsalandan ba. In ji babban kwamandan na IRGC.

Salami ya jaddada cewa, “Mu ba al’ummar da ke gudanar da ayyukanta cikin sirri ba ne; a maimakon haka, muna yin komai a bisa doka da oda da kuma kiyaye ka’idoji na duniya, kuma komai namua  fili yake, kuma lokacin da muka dauki matakin soji a kan Isra’ila ba mu boye ma kowa ba kamar yadda duniya ta sheda hakan a cewar janar Salami.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • WSCIJ Ta Naɗa Farfesa Umaru Pate A Kwamitin Amintattu
  • Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka
  • Yemen Ta Cilla Makamai Kan Kataparen Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Yaki Na Amurka A Tekun Red Sea
  • Munanan Hare-hare  Sojojin HKI A Gaza Da Safiyar Yau Talata Sun Yi Sanadiyyar Shahadar Fiye Da Falasdinawa 200
  • Adadin Shahidan Falasdinawa A Gaza Ya Karu Da 14 A Jiya Lahadi Saboda Hare-Haren Sojojin HKI
  • Kungiyar Ansarullah Ta Ce Keta Hurumin Kasar Da Amurka Ta Yi Zai Gamu Da Maida Martani
  • Kasar Habasha Ta Bukaci Kasashen Afirka Su Bunkasa Ciyar Yaki Da Cututtuka CDC Da Kungiyar
  • IRGC: Iran ba za ta fara yaki ba amma za ta mayar da martani ga duk wata barazana
  • Hizbullah ta yi Allah wadai da harin Amurka da Birtaniya a kan Yemen