Aminiya:
2025-03-19@15:17:32 GMT

Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq

Published: 19th, March 2025 GMT

Fitaccen jarumi a Masana’antar Kannywood Sadik Sani Sadik ya ce shi ba fadakarwa yake yi a fim ba, inda ya ce neman kuɗi kawai yake yi.

Jarumin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Gidan Rediyon Freedom, inda a ciki yake cewa ba tarbiyya yake koyarwa ba, ballantana a ce yana bata tarbiyyar.

Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

A cewarsa, “Ni ban ce ina fadakarwa ba.

Ni Sadik Sani Sadik ban ce ina fadakarwa ba. Ban ce ina tarbiyyantarwa ba.

“Tarbiyya ana ba yaro daga gida ne, fadawarka kuma malamai ne ke yi. Ni ba mai fadakarwa ba ne. Ni mai neman kudi ne.

“Shi fim ba ya da yare, ba ya da addini, saboda haka ya danganta da yanayin da za ka gudanar da fim dinka.

“Idan danka ya kalli fim dina, tarbiyyarsa ta tabu, ba daga ni ba ne, daga kai ne. Idan ma danka bai kalli fim din Hausa ba, zai kalli na Indiya da wakokin Turawa da ake rungume-rungume.

“Ni kuma a fim din Hausa idan na taba hannun mace ya zama abin magana, ban isa ba wallahi.”

Game da mata sun fi maza samun kudi, sai ya ce, “Wasu matan sun fi wasu mazan kudi.

“Kudi ai sirri ne ba wai ka ga mutum ya hau motoci ko ya sanya gwala-gwalai ba ne.

“Ya danganta ne, wani idan yana da dubu daya sai ka gane, wani kuma yana da miliyan daya, amma ba za ka gane ba.”

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da da Faransanci

Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya.

A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ɗan Afirka da yake da ‘ya’ya 104 da jikoki 144
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [11]
  • Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da Faransanci
  • Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da da Faransanci
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [10]
  • Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano
  • Mayakan “Jubhatun-Nusrah’ Na Kasar Syria Sun Kai Hari Akan Iyakar Kasar Leabnon
  • Ba Don Tarbiyantar Da Mutane Nake Yin Fim Ba -Amina Shehu Lulu