Wata Kungiyar Agaji Mai Zaman Kanta, Ike Odoeme Foundation, ta taimaka wa yankuna biyu a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, ta hanyar haka rijiyoyin burtsatse guda bibbiyu a kowane yanki.

A yayin kaddamar da ayyukan a kauyukan Facawa da Riniyal da ke  Ringim, jami’ar shirye-shirye ta gidauniyar, Miss Suzie Agas, ta bayyana jin dadinsu na yin tasiri a rayuwar al’ummar yankin.

 

A cewarta, wannan aikin yana tabbatar da kudirin gidauniyar na tabbatar da cewa kowace al’umma tana da damar samun tsaftataccen ruwa, ba tare da la’akari da matsayinta ko inda take ba.

Suzie Agas ta jaddada cewa ruwa yana da matukar muhimmanci ga kiwon lafiya da ci gaban tattalin arziki, amma abin takaici, al’ummomi da dama na fuskantar kalubale wajen samun tsaftataccen ruwa.

Ta kara da cewa rashin ruwa mai tsafta yana haddasa cututtukan da ake dauka ta ruwa, yana hana mutane yin ayyuka da kyau, kuma yana rage damarmakin yaran makaranta don mayar da hankali kan karatunsu.

Suzie ta gode wa hukumomin karamar hukumar Ringim bisa goyon baya da hadin kai da suka bayar wajen tabbatar da tsaro da aminci a lokacin aikin.

Ta kuma roki al’ummomin Facawa da Riniyal da su kula da rijiyoyin, don gujewa samun matsala.

A nasa jawabin yayin kaddamar da rijiyoyin, hakimin Sankara, Alhaji Yusi Ahmed, ya tabbatar da cewa wadannan al’ummomi sun shafe shekaru da dama suna fama da karancin ruwa.

Ya ce ko da yake an taba samar da rijiyoyi a wadannan yankuna, rashin kulawa da su ya sa suka lalace.

Ya bukaci mazauna yankin da su dauki nauyin kula da rijiyoyin domin su dade suna amfani da su fiye da wadanda aka samar a baya.

Shi ma da yake nasa jawabi, Shugaban Karamar Hukumar Ringim, Alhaji Badamasi Dabi, ya jinjinawa gidauniyar bisa jajircewarta wajen tabbatar da kammala aikin.

Ya bayyana cewa karamar hukumar Ringim tana da cikakken shirin yin hadin gwiwa da kungiyoyin agaji domin ci gaban al’umma.

Bayan haka, gidauniyar ta rabawa al’ummar buhunan shinkafa.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana godiyarsu bisa wannan aikin, inda suka ce hakan ya rage wahalar da ‘ya’yansu ke fuskanta wajen yin doguwar tafiya domin samo ruwa.

 

Usman Muhammad Zaria 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda.

Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi

Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar.

‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’

Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya kasance yana aiki ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce duk da tankiyar siyasa, ya ci gaba da gudanar da aiki don tabbatar da tsaro da inganta rayuwar mutanen Jihar Ribas.

Ya ƙara da cewa bayan shugaban ƙasa ya shiga tsakani domin kawo zaman lafiya, ya kiyaye duk yarjejeniyar da aka cimma, ciki har da karɓar kwamishinonin da suka yi murabus a baya.

Bayan haka, gwamnan ya ce ya amince da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke domin mayar da jihar kan turbar da doka da oda suka tanadar.

‘Majalisar dokokin Ribas ta hana ruwa gudu’

Gwamnan ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatinsa ta yi domin samar da zaman lafiya, ’yan majalisar dokokin jihar sun kawo cikas.

Ya ce yana aiki ne don tabbatar da an kare dimokuraɗiyya da ci gaban mutanen jihar amma majalisar ta riƙa hana ruwa gudu.

A cewarsa, duk da saɓanin siyasa da ake fama da shi, gwamnatinsa na biyan albashin ma’aikata tare da aiwatar da manyan ayyuka don ci gaban jihar.

Fubara ya bayyana cewa duk da ƙalubalen siyasar, ya tabbatar da jihar na cikin kwanciyar hankali kuma babu wata barazanar tsaro da ake fuskanta.

A ƙarshe Fubara ya buƙaci mutanen jihar da su zauna lafiya tare da guje wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace don kare dimokuraɗiyya da tabbatar da ci gaban jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas
  • HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano
  • Gidauniyar Dangote Ta Bai Wa Jihar Bauchi Tallafin Buhun shinkafa 25,000
  • Hukumar Alhazan Jihar Jigawa Ta Ware Kujeru 54 Ga Malamai Da Jami’an Kananan Hukumomi
  • MDD ta bukaci masu ruwa da tsaki a Yemen da su kai zuciya nesa
  • Iran ta kuduri aniyar yin hadin gwiwa da hukumar IAEA
  • Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya
  • Ministan Noma Na Gambiya: Hadin Kan Gambiya Da Sin A Fannin Aikin Gona Ya Haifar Da Sakamako Mai Kyau
  • IRGC: Iran ba za ta fara yaki ba amma za ta mayar da martani ga duk wata barazana