Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas
Published: 19th, March 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin Mai Kula da Jihar Ribas.
An rantsar da shi ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin RibasNaɗin ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Talata, bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin Jihar.
Bayan ayyana dokar ta-ɓacin, Tinubu ya sanar da cewa Vice Admiral Ibas ne zai jagoranci jihar na tsawon watanni shida.
Yayin jawabinsa, Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa dokar ta-ɓacin ba ta shafi ɓangaren shari’a ba, kuma kotuna za su ci gaba da gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu
Gwamnatin Tarayya ta haramta amfani da wata sabuwar waƙar da ke sukar Shugaba Bola Tinubu a dukkanin kafofin labarai na rediyo da talabijin a faɗin ƙasar.
Waƙar da mawaƙi Eedris Abdulkareem ya fitar a baya-bayan nan mai suna“ Tell Your Papa”, ta soki yadda Shugaba Tinubu ke gudanar da tattalin arzikin Nijeriyar.
An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina An kama mutum 8 kan faɗan daba a KanoThe lyrics are addressed to Tinubu’s son, calling on him to let his father know “people are dying” from economic hardship as well as continued insecurity from armed groups.
Baitocin waƙar da ke ɗauke da kira ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu, sun buƙaci ya isar wa mahaifinsa saƙon cewa ’yan Nijeriya na fama da matsanancin ƙunci na tattalin arziki da kuma matsalar tsaro.
Sai dai Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai a Najeriya NBC, ta shaida wa kafofin labaran ƙasar cewa waƙar ta saɓa ƙa’ida da ma taɓa “mutuncin gwamnati.”
Tuni dai mawaƙi, Eedris Abdulkarim, ya mayar da martani, inda ya buƙaci magoya bayansa su saurari waƙar ta hanyoyin da kafar Intanet ta bayar da dama.
Abdulkareem ya wallafa a shafinsa na zumunta cewa, faɗa wa gwamnati gaskiya ko sukar gyara kayanka a kullum laifi ne a Nijeriya.
Shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu a ƙasar dai sun gamu da zanga-zanga musamman kan tsadar rayuwa da man fetur.