Aminiya:
2025-04-13@11:00:45 GMT

Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe

Published: 19th, March 2025 GMT

Rahotanni sun nuna cewa gobara ta kashe yara uku tare da jikkata wasu 13 a ƙauyuka tara na Jihar Yobe, tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2025.

Gobarar ta kuma lalata gidaje 86, inda ta bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba.

Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq

Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Yobe (YOSEMA), Dokta Mohammed Goje, ya bayyana cewa rashin kula da wutar lantarki, amfani da gas, ƙonewar daji, da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, ke haddasa yawan gobara a jihar.

Ya ce lamarin ya fi shafar yankunan Damaturu, Gulani, da Yusufari, inda mazauna ke kokawa kan asarar da suka yi.

Domin magance matsalar, hukumar YOSEMA ta fara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kauce wa gobara.

Haka kuma, sun kafa kwamitoci da za su taimaka wajen kare lafiyar al’umma, musamman a lokacin rani da hunturu.

Dokta Goje ya ce hukumar, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta jihar, za su ɗauki matakan hana ƙone daji da kuma bin ƙa’idojin zubar da shara domin rage haɗuran gobara.

A gefe guda, Gwamna Mai Mala Buni ya umarci hukumar YOSEMA da ta tantance ɓarnar da gobarar ta yi, domin sanin irin taimakon da waɗanda lamarin ya shafa suke buƙata.

Gwamnan ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa za a tallafa musu.

A halin yanzu, hukumomi na ci gaba da faɗakar da jama’a kan muhimmancin kiyaye dokokin kare gobara domin gujewa aukuwar irin wannan iftila’i a gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gobara gwamnati rasuwa shara yara

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu

Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya ce kasashen wamma suna son kebe kansu da fasahar nukliya a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Eslamu shugaban hukumar AEOI yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kafa a kasar Iran kuma ba wanda ya isa ya kauda shi. Sabanin abinda kasashen yamma suke so na hana sauran kasashen duniya mallaka fasahar nukliya, da kuma dogara da su kadai, su bada abinda suka ga dama ko  su hana gaba daya.

Ya ce JMI ta wuce wasu kasashen yamma a ayyuka da kuma sani da sarrafa makamashin Uranium, wanda ya tada hankalin wadannan kasashe, kuma suke sun han awasu kasashen duniya bin sawun kasar Iran na zama yentattu a wannan fage.

Islami ya kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kai wani matsayinda yana taiamakawa sauran kamfanoni na cikin gida ba tare da bukatar dogaro da kwararru ko kuma taimakon kasashen waje ba. Ya ce a halin yanzu iran na samar da wutan lantarki mai karfin magewats 20,000 tare da Makamashin Nukliya.

     

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ta kai ƙarar kamfanin jirgi da fasinja kan kukan yaro
  • Bam Ya Hallaka Mutane 8, Wasu da Dama Sun Jikkata A Borno
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Mutane Da Yawa Sun Jikkata Bayan Fashewar Bam A Wata Kasuwa A Ikeja
  • Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu
  • An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi 
  • An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato
  • Gobara Ta Ƙone Shaguna 12 A Kasuwar Siminti Ta Oyo
  • Za a mayar da tubabbun ’Yan Boko Haram cikin al’umma – Gwamna Buni
  • Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe