Leadership News Hausa:
2025-04-14@17:56:15 GMT

Matatar Dangote Ta Dakatar Da Sayar Da Man Fetur A Naira

Published: 19th, March 2025 GMT

Matatar Dangote Ta Dakatar Da Sayar Da Man Fetur A Naira

Matatar man Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a naira. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da matatar ta aika wa abokan huldarta a yammacin ranar Laraba. ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC A cikin sanarwar, Matatar ta ce, wannan matakin na wucin gadi ne, inda ta bayyana dalilin da ya sa aka dauki matakin domin samar da daidaito tsakanin farashin danyen mai da aka siyo da Dala da kuma na Naira.

“Muna so mu sanar da ku cewa, matatar man Dangote ta dakatar da sayar da man fetur a Naira na wani dan lokaci domin kauce wa rashin daidaito tsakanin danyen man da ke wurinmu wanda a halin yanzu ke kan farashin dalar Amurka. “Ya zuwa yanzu, cinikin man fetur da muke samu a Naira ya zarce na danyen man da muka samu a farashin Naira, a sakamakon haka, dole ne mu daidaita kasuwancinmu na dan lokaci. “Muna ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da bai wa ‘yan kasuwannin Nijeriya kayayyakinmu mai inganci da zarar mun samu danyen man fetur daga kamfanin NNPC, nan take za mu dawo da cinikin man fetur a Naira”.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: man fetur a Naira

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji 16 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Filato

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Ya Gana Da To Lam Na Vietnam
  • Sojoji Sun Ceto Fasinjoji 16 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Filato
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Siyo Tan Tan 360 Ga Manoma
  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Matakin Kare-Karen Harajin Fito Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar
  • Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
  • Sin: Idan Har Amurka Na Son Tattaunawa, Ya Zama Wajibi Ta Dakatar Da Aiwatar Da Matakan Gangaci
  • ‘Yan Boko Haram Na Ci Gaba Da Mamaye Sassan Jihar Borno -Zulum
  • Basukan Da Nijeriya Ke Biya Sun Karu Zuwa Naira Tiriliyan 13