Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Gwamnan Rikon Kwarya Na Jihar Rivers
Published: 19th, March 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantad da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, da wasu hadiman Shugaban Kasa sun halarci wannan gajeren bikin rantsuwar da aka gudanar a Fadar Gwamnati a ranar Laraba.
Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers a ranar Talata, 18 ga Maris, domin magance rikicin siyasa wanda ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisar dokokin jihar, duk da hukuncin da Kotun Koli ta yanke.
A yayin ayyana dokar ta-baci na tsawon watanni shida, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa halin rashin tsaro da matsin lamba na siyasa a jihar ya tilasta masa shiga tsakani domin hana tabarbarewar doka da oda gaba daya.
Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, wanda aka haifa a ranar 27 ga Satumba, 1960, yana da kwarewa wajen yi wa kasa hidima.
An ba shi mukamin sub-lieutenant a Sojin Ruwa na Najeriya a shekarar 1983, inda ya rike mukamai daban-daban har zuwa lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi Shugaban Hafsan Sojin Ruwa a watan Agusta na 2015. Ya rike wannan mukami har zuwa 2021.
Bayan ritayarsa daga aiki, Shugaba Buhari ya naɗa shi Jakadan Najeriya a Ghana, inda ya yi aiki daga 2021 zuwa 2023.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Ribas
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna da mataimakinsa da daukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da ayyana dokar ta-baci a Jihar.
Tinubu ya kuma ayyana Ete Ibas a matsayin Gwamnan Rikon Jihar Ribas, a yayin jawabinsa ga ’yan Najeriya