Nijar, Burkina Faso da Mali sun fice daga kungiyar kasashe renon Faransa
Published: 19th, March 2025 GMT
Kasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali kowannensu sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashe renon faransa ta (OIF).
Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar a ranar Litini, yayin da Mali ta bi sahu a ranar Talata, aa daidai lokacin da ake raya makon kungiyar.
Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar Laouali Labo, a wata wasika da ya aikewa jakadun kasar ya ce: “Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar ficewa daga kungiyar ta OIF.
Nijar dai na daga cikin kasashen da suka asassa kungiyar ta OIF, wacce aka kafa a Yamai babban birinin kasar a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1970, kuma tsohon shugaban kasar Dojori Hamani na waccen lokacin na daga cikin jagororin da suka kafa kungiyar.
To saidai dangankata ta yi tsami tsakanin faransa da sojojin dake mulki a kasashen guda uku a baya bayan nan.
Kungiyar ta OIF, “maimakon tallafawa wadannan kasashe wajen cimma manufofin raya al’ummarsu, (…) ta kauce wa hanya inda ta sanya siyasa a cikin lamuranta,” in ji ministocin harkokin wajen kawancen kasashen guda uku na Sahel a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a yammacin jiya Talata.
Kungiyar ta OIF, da ta hada kasashe da gwamnatoci 93, manufarta ita ce inganta harshen Faransanci da raya al’adu, don ƙarfafa zaman lafiya, da dimokuradiyya da ‘yancin dan adam, don tallafawa ilimi, horo da bincike, da kuma inganta hadin gwiwar tattalin arziki don samun ci gaba mai dorewa.
Sai nan da watanni shida masu zuwa ne ficewar kasashen za ta tabbata.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kungiyar ta OIF daga kungiyar
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen
Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa jiragen yakin kasar ta Amurka sun kai hare-hare har 5 a kan makarantar koyon sana’o’ii na Al-sawma da ke lardin Al-Bayda a jiya Asabar .
Labarin ya kara da cewa makarantar ita ce babbar makaranta a yankin, kuma cibiyar ilmi mafi girma. Har’ila yau labarin ya bayyana cewa jiragen yakin kasar ta Am,urka sun kai hare-hare har guda 3 a kan garin Al-Sahleen daga cikin yankunan Kitif da kuma Al-Bogee daga cikin lardin Sa’ada.
Labarin ya kara da cewa wannan yankin yana daga cikin yankunan da ake fafatawa da sojojin Amurka, kuma suna yawaita kan hare-hare a cikinsa.