Iran : hare-haren Isra’ila a Gaza ci gaba da kisan kare dangi ne
Published: 19th, March 2025 GMT
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baghaei, ta yi kakkausar suka ga sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza, yana mai bayyana su a matsayin “ci gaba da kisan kiyashi da share wata al’umma a yankin da aka yi wa kawanya.
Baghaei ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, sa’o’i bayan harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan Falasdinawa da suka hada da mata da kananan yara.
Ya ci gaba da cewa, Amurka ce ke da alhakin kashe-kashen da ake yi a Gaza, yana mai cewa, ana kai hare-haren na Isra’ila ne da tare da goyan bayan Washington.
Baghaei ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu, tare da dakatar da laifukan yaki da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza, wadanda ake aiwatar da su tare da cikakken goyon bayan Amurka, Birtaniya da sauran kasashen yammacin duniya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya kuma ce rashin yin magana a fili kan keta dokokin kasa da kasa da Isra’ila ke yi, zai gurgunta tsarin shari’a na ka’idojin da aka kafa bisa kundin tsarin mulkin MDD, yana mai gargadi kan illar da irin wannan yanayi ke haifarwa ga zaman lafiya da tsaro a duniya.
Baghaei ya kuma bayyana irin nauyin da al’ummar musulmi ke da shi, inda ya bukaci kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ta dauki kwararan matakai na gaggauta gurfanar da shugabannin Isra’ila a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC), da kuma dakatar da bayar da tallafin makamai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa: Ba ta neman tada tashin hankali tsakaninta da Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Samuel Werberg ya bayyana cewa: Kasarsa ba ta neman kara ruruta wutar rikici da Iran, yana mai jaddada cewa har yanzu kofar diflomasiyya a bude take, duk kuwa da kakkausar murya da Amurka ta yi na kin amincewa Iran ta mallaki makamin nukiliya.
Werberg ya kara da cewa; Za su ci gaba da riko da siyasar matsin lamba da nufin dakatar da ci gaba a shirin nukiliyar Iran.
Kakakin na Amurka ya bayyana cewa, “Dole ne Iran ta nuna kyakkyawar niyyarta kafin ta yi magana kan duk wata nasara da za a samu.