Hare-haren Isra’ila sun yi sanadin shahadar falasdinawa kusan 1,000 a cikin sa’o’I 48
Published: 19th, March 2025 GMT
Rahotanni daga Gaza na cewa hare haren Isra’ila a baya bayan nan sun yi sanadin shahadar mutane kusan 1,000 a baya bayan nan wanda ke nuna irin girman barnar da gwamnatin sahayoniyan ke aikatawa a zirin.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce sabon danyen aikin da Isra’ila ta yi ya kai ga kashe akalla mutane 970 cikin sa’o’i 48.
Wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar ta bayyana cewa, hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kaddamar a ranar Talata, sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 970.
Wasu rahotanni na daban ce mutane 356 ne suka mutu a harin da aka kai ta sama, a cikin sa’a huda sannan akalla Falasdinawa 1,000 ne suka samu raunuka.
Wani babban jami’in Hamas ya shaidawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa hare-haren na Isra’ila na nufin cewa Isra’ila ta kawo karshen tsagaita bude wuta a Gaza da aka fara a ranar 19 ga watan Janairu.
Mohammed Zaqout, babban darektan asibitocin Gaza, ya yi kira ga kasashen duniya da su shiga tsakani tare da tilastawa Isra’ila ba da damar samar da magunguna a cikin yankin.
Mata da yara da dama na daga cikin wadanda aka kashe
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce akalla Falasdinawa 61,700 ne aka tabbatar da mutuwarsu tare da jikkata 112,041 a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sayyid Husi: Idan Amurka Ta Ci Gaba Da Kai Mana Hare-hare To Muna Da Hanyoyin Gasa Mata Aya A Hannu
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi ya bayyana cewa; Matukar Amurka ta ci gaba da kai wa Yemen hare-hare, to suna da hanyoyi da za su iya gasa mata aya a hannu masu yawa.
Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishara da yadda dubun dubatar mutanen Yemen su ka fito a cikin birnin San’aa da kuma sauran biranen kasar domin raya da tunawa da rana da aka yi yakin Badar, yana mai cea; hakan yana a matsayin wani sako ne zuwa Amurka da Isra’ila, kuma tabbas idan su ka ci gaba da kai wa Yemen hari, to muna da zabi na hanyoyin da za mu yi amfani da su domin dandana musu kudarsu.
Sayyid Husi wanda ya gabatar da jawabin dararen Ramadan mai alfarma ya kara da cewa; Sakon mutanen Yemen da su ka fito a Litinin din nan 17 ga watan Ramadana shi ne; Ba za mu taba barin abokan gaba Isra’ilawa su ci gaba da cutar da al’ummar Falasdinu, a karkashin goyon bayan Amurka ba.”
Shugaban na Ansarullah ya kuma yi Magana akan yadda abokan gaba Isra’ilawa suke ci gaba da hana shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza, wanda babban laifi ne da bai kamata a yi shiru a sa musu idanu ba.”
Haka nan kuma ya kara da cewa; Matakin da mu ka dauka na farko, amma idan har aka ci gaba, yunwa ta kara takurawa Falasdinawa, to matakin da za mu dauka zai fi na yanzu.”
Danagne da martanin da su ka kai wa jigin dakon jiragen yaki na Amurka a tekun “Red Sea”, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishar da yadda jiragen yakin na Amurka su ka kara yin nisa zuwa kilo mita 1300, domin tsoron hare-haren sojojin Yemen.