Sabon Kawancen Jihohin Arewacin Najeriya Da Kamfanonin Sin Zai Fa’idantar
Published: 20th, March 2025 GMT
A dunkule, ayyukan da wadannan kamfanoni za su gudanar sun kunshi samar da wadataccen takin zamani da fasahar noma ta zamani, da dabarun sarrafa takin gargajiya da fasahar kiwo mafi dacewa da jihar. Haka nan, kawancen nasu zai hada har da amfani da fasahohin zamani wajen kyautata sha’anin tsaro, da harkokin sufuri da bangaren hidindimun jama’a, da sauran dabaru da tsare-tsare na kwarewar aiki da za a samar a jihar.
Hakika wannan kawance zai fa’idantar sosai saboda yadda yankin na arewa ya kwashi tsawon wasu shekaru yana kaka-ni-ka-yi da matsalolin dake tarnake ci gabansa sakamakon mummunar matsalar tsaro musamman ma a jihar Zamfara wadda ta zama babbar tungar ’yan bindiga.
Kwararru a fannin sha’anin tsaro, sun sha nanata cewa matukar ana so a magance matsalar tsaron da ta hana arewacin Najeriya sakat dole sai an hada da magance zaman kashe wando, da bunkasa tattalin arziki da kuma samar da na-gartaccen ilimi.
Sabon yunkurin jihohin arewa na kulla kawance da kamfanonin Sin babu shakka zai bude kofofin karfafa tattalin arzikin yankin wanda Allah ya albarkace shi da kasar noma mai kyau fiye da sauran sassan Najeriya, sannan ga tarin albarkar yawan jama’a, da albarkatun sarrafa sabbin makamashi, domin kamfanonin Sin suna da kwarewar aiki da dimbin ayyuka na fasahar zamani ta yadda suke iya sarrafa albarkatu kalilan a samar da amfani mai yawa. Sannan suna da karfin zuba jari fiye da yadda ake zato, domin ko a watan Satumban 2024, gwamnatin jihar Neja da ke arewacin Najeriya ta rattaba hannu da wasu kamfanonin Sin guda biyu –COVEC da CREC a kan kwangilar dala miliyan 684 domin gudanar da ayyukan gona na musamman a jihar.
Tabbas, jihohin sun dauki hanya mai kyau da za ta fa’idantar, fatana shi ne a wayi gari yankin arewa ya dawo da martabarsa ta ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma.(Abdulrazaq Yahuza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yadda Ake Tuwan Amala Da Miyar Uwaidu
Ga kuma yadda ake sarrafawa:
Da farko, a zuba ruwa a tukunya a sa a wuta domin ya tafasa.
A rage wuta kadan, sannan a zuba garin alabo a hankali cikin ruwan da ke tafasa, ana juyawa da muciya ko cokali ko leda mai kauri don kada ya yi kolalla.
A ci gaba da juyawa har sai ya hade sosai kuma ya zama mai laushi.
Idan yana da kauri sosai, sai a kara dan ruwan zafi kadan wanda dama kin rage, kuma a ci gaba da juyawa har sai ya yi laushi.
A rufe shi na ‘yan mintuna kafin a sauke.
Sai kuma yadda ake miyar Uwedu:
Iata ma ga abubuwan da ake bukata domin hada ta:
Ganyen Ewedu (fresh leabes)
Kanwa ko potash (dan kadan),Gishiri, Magi, yaji
Sai kuma yadda ake hadawa:
A gyara ganyen Ewedu, a wanke su da kyau.
Sannan a zuba ruwa kadan a tukunya, a sa kanwa ko potash, a sa a tafasa.
Idan ruwan ya tafasa, sai a zuba ganyen uwedu, a dafa na kimanin minti 5–7. A sauke, sannan a daka a cikin turmi ko a murza da blender idan ana so ya zama ya yi laushi. Sai a mayar da shi tukunya, a sa gishiri da maggi da yaji idan ana so, a dafa na minti kadan sai a sauke.
A ci dadi lafiya.
Za’a dan iya zuba miyar ja ko nama ko ganda ko kifi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp