Leadership News Hausa:
2025-03-20@11:38:50 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [12]

Published: 20th, March 2025 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [12]

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [10] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [9]

Fashin Baƙi:

Ibn Juzai, ya bayyana nau’ikan rai uku da suka shafi halayyar ɗan’adam, bisa koyarwar addinin Islama. Waɗannan nau’ikan rai suna da nasaba da matsayin mutum a cikin halayensa da alaƙarsa da Allah.

Ga cikakken bayani kan kowanne daga cikinsu:

1. Rai Mai Umarni da Mummuna (النَّفْسُ الأَمَّارَةُ بِالسُّوءِ): Wannan ita ce zuciyar da take yawan umartar mai ita da aikata sharri da mugunta, da saɓo. Allah Ya ambaci irin wannan rai a cikin Alƙur’ani inda Ya ce:” Ba kuma ina wanke kaina ba ne. Shakka babu ɗabi’ar rai ce ta umurci mutum da yin mummunan abu, sai fa wanda Ubangiji Ya yi wa jin ƙai. Lalle Ubangiji Mai gafara ne Mai jin ƙai” Suratu Yusuf aya ta 53.

Irin wannan rai tana da alaƙa da sha’awa, da son zuciya, da rinjayen Shaiɗan a kanta. Duk wanda yake a wannan matsayi, yana yawan aikata laifi ba tare da jin kunya ba. Sai dai idan Allah Ya yi masa rahama, zai farka daga halinsa ya nemi gafara ya tuba.

Alamomin Rai Mummuna: Yawan aikata zunubi ba tare da nadama ba.
Jin daɗi da mugunta da zalunci.
Rashin kulawa da umarnin Allah da hani.
Bin son zuciya da jin daɗin duniya fiye da lahira.

Hanyoyin Gyara Irin Wannan Rai:

● Neman gafarar Allah akai-akai.
● Yawan ambaton Allah (zikiri) don rage rinjayen sha’awa.

●Yin hijira daga munanan abokai ko yanayi.
● Cusa wa rai ƙaunar ibada da karatun Alƙur’ani.

2. Rai Mai Yawan Zargin Kanta (النَّفْسُ اللَّوَّامَةُ):
Wannan ita ce zuciyar da take tsawatar da mai ita a lokacin da ya aikata kuskure,ko zai aikata shi. Wannan nau’in rai yana matakin tsaka-tsaki tsakanin mugunta da kyautatawa. Allah Ya ambaci wannan rai a cikin Alƙur’ani, inda Ya ce:” Ina rantsuwa da rai mai yawan zargin kanta.” Suratul Ƙiyama aya ta 2.

Mutumin da yake da wannan rai yana aikata laifi amma daga baya zuciyarsa tana yi masa tir, tana sa shi jin nadama. Wannan nadama ita ce take jawo tuba da gyara hali.

Alamomin Rai Mai Yawan Zargin Kanta:

● Yawan jin laifi da nadama bayan aikata kuskure.
● Farkawa daga barci na gafala idan aka yi laifi.
●Rashin kwanciyar hankali yayin aikata haram.
● Son gyara hali da tuba.

Hanyoyin Ƙarfafa Rai Mai Yawan Zargin Kanta:

● Cusa wa zuciya son Allah da Manzonsa.
● Taimaka wa rai da kyakkyawan abokai.
● Rayuwa a cikin yanayi mai tsafta da ibada.
● Yawan karanta tarihin mutanen kirki don yin koyi da su.

3. Rai Mai Nutsuwa (النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ): Wannan ita ce zuciyar da ta samu cikakken natsuwa da yarda da hukuncin Allah. Wannan mataki ne mafi girma a cikin halayyar rai. Allah Ya ambaci irin wannan rai a Alƙur’ani inda Ya ce:” Ya kai wannan rai mai nutsuwa. Ka koma zuwa ga Ubangijinka kana mai yarda da sakamako abin yarda. Don haka, ka shiga cikin bayina. Ka kuma shiga Aljannata.” Suratul Fajri aya ta 27-30.

Wannan matakin na rai yana ga mutanen da suka sami cikakkiyar ɗa’a da biyayya ga Allah da Manzonsa (S.A.W). Sun tsarkake zukatansu daga son zuciya, da hassada, da riya, da zalunci. Duk wata fitina da ta zo masu, sun yarda da cewa ƙaddarar Allah ce, don haka ba sa firgita ko damuwa.

Alamomin Rai Mai Nutsuwa:

● Tsananin ƙaunar Allah da Manzonsa fiye da komai.
● Cikakkiyar yarda da ƙaddara, mai daɗi ko akasin haka.
● Jin daɗin ibada da guje wa sharri.
● Kyautatawa ga mutane ba tare da neman lada a duniya ba.
● Jin daɗin rayuwa ko da an sami wahala.

Hanyoyin Samun Rai Mai Nutsuwa:

● Yawaita karatun Al-Qur’ani da nazarin ma’anoninsa.
● Yin addu’a don tsarkake zuciya daga cututtukan rai.
● Yawaita tunani a kan lahira da rayuwar gaskiya.
● Gujewa duniya da halayenta marasa amfani.

Waɗannan nau’ikan rai suna nuni da matakin da mutum yake a cikin bautar Allah. Duk wani mai imani yana ƙoƙarin tashi daga rai mai umurni da mummuna zuwa rai mai yawan zargin kanta, sa’an nan zuwa rai mai nutsuwa. Wannan tafiya tana buƙatar dagewa da ibada, sabo da zuciya na da ƙarfi wajen rinjayar hali.

Ibn Juzai Allah Ya yi masa rahama ya bayyana waɗannan matsayin domin su zama ginshiƙin gyara hali da kyautata rayuwa ta ibada. Duk wanda yake aiki da wannan koyarwar, zai iya cimma babban matsayi na kusanci da Allah, wanda a ƙarshe zai kai shi ga samun dacewa da rahama a duniya da lahira.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau

Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau.

Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja.

Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji

Wakilinmu ya ruwaito cewa a yanzu ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada ne zai gaje shi a wannan kujera
ta hakimanci.

Farfesa Ango Abdullahi yana ɗaya daga cikin mazan jiya da suka yi ragowa a Nijeriya.

Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ɗaya ne daga cikin dattawan da al’umma suke buƙata musamman a wannan zamani.

Yana ɗaya daga cikin masu bayyana ra’ayin su a kowanne irin yanayi don jawo hankalin shugabanni da al’ummomi da nufin kyautata rayuwa.

Kazalika, Farfesa Ango Abdullahi shi ne na biyar a tarihin cikin jerin waɗanda suka riƙe muƙamin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tuni dai Masarautar Zazzau ta bayyana Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada wadda ƙani ne ga shi Farfesa Dahiru Ango Abdullahi a matsayin sabon Magajin Rafin Zazzau.

Sai dai masarautar ta ce zuwa nan gaba kaɗan za ta fidda ranar da za a yi bikin naɗin sabon Magajin Rafin Zazzau.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HKI Ta Tilastawa Iyalai 10 Ficewa Daga Gidajensu A Sansanin ‘Yan Hijira Na Nabilus
  • DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [11]
  • Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau
  • Gidauniyar Dangote Ta Bai Wa Jihar Bauchi Tallafin Buhun shinkafa 25,000
  • Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja
  • Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da Faransanci
  • Nijar Ta Fice Daga Kungiyar Kasashen Da Ke Amfani Da da Faransanci
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [10]