Aminiya:
2025-03-20@16:38:09 GMT

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari

Published: 20th, March 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A yau, mutane da dama sun fahimci muhimmancin koyan sana’a wajen dogaro da kai, maimakon dogaro da aikin gwamnati ko na kamfani.

Sai dai ana zargin wasu masu masu sana’ar hannu, musamman teloli, da rashin cika alƙawari.

NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya

A mafi yawan lokuta, ana samun matsala da su, musamman a lokutan bukukuwa, inda suke kasa kammala ɗinkin kayan da aka ba su ko suka yi alƙawari.

Shirin Najeriya A Yau, zai yi nazari kan dalilan da suka sa teloli ke kasa cika alƙawari da yadda hakan ke shafar kwastomomi.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwastomomi Rashin Cika Alƙawari

এছাড়াও পড়ুন:

Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa

Bayan shafe kwanaki 40 har yanzu waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriy a(NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya ba su sako shi ba duk da cewa an biya kuɗin fansa.

Rahotanni sun nuna cewar an biya maƙudan kuɗaɗe don ganin an sako Janar Tsiga, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 5 ga watan Fabrairun da ya gabata a Ƙaramar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.

Wata 11 da tuɓe rawanin wasu sarakuna a Sakkwato Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata

Wata majiya ta kusa da iyalansa ta ce bayan kai kuɗin, sai da aka shafe mako guda kafin ’yan bindigar suka sake tuntuɓar iyalansa, inda suka haɗa su ta waya, sannan kuma suka sake neman ƙarin wasu kuɗaɗe.

“Saboda wasu dalilai gaskiya ba zan faɗi adadin kuɗin da aka biya ba amma kuɗaɗe ne masu yawan gaske,” a cewar majiyar.

Da farko dai waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Janar ɗin, sun buƙaci a ba su naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansa, sai dai an ci gaba ta tattaunawa da su.

Wasu bayanai na cewa akwai yiwuwar waɗanda suka yi garkuwa da shi sun sauya masa matsugunni.

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya ACF da kuma ta Dattijan Jihar Katsina KEF, sun buƙaci gwamnatin da kuma rundunar sojojin ƙasar, su matsa ƙaimi wajen ganin an kuɓutar da shi da sauran mutanen da aka yi garkuwa tare da su.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya: Ana Fargabar Sake Tashin Farashin Fetur Bayan Dangote Ya Daina Sayar Da Mai A Naira
  • Mutane Fiye Da 30 Ne Suka Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Dawkar Gas Ta Yi Bindiga A Abuja Na Tarayyar Najeriya
  • Jakadan Amurka Ya Ziyarci Sarkin Zazzau Domin Karfafa Alakar Amurka Da Najeriya
  • A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya
  • Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja
  • Sabon Kawancen Jihohin Arewacin Najeriya Da Kamfanonin Sin Zai Fa’idantar
  • Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa
  • Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan