’Yan bindiga sun sace shugaban kasuwar kayan miya ta Akinyele a Oyo
Published: 20th, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga sun kai hari Kasuwar Kayan Miya ta Akinyele, kusa da Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, inda suka sace Shugaban Kasuwar, Alhaji Usman Yako.
Bayanan da muka samu daga shugabannin kasuwar sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na dare, jim kadan bayan an idar da sallar Magriba.
Mataimakin Shugaban Kasuwar, Alhaji Abdul’aziz Abdulwasi’u (Dan Kashi), ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Bayan na koma gida domin shan ruwa, sai yarona ya kira ni ta waya ya shaida min cewa wasu mutane ɗauke da bindigogi sun shigo kasuwa suna harbe-harbe.
“Sun tilasta Shugaban Kasuwa Alhaji Usman Yako ya fito daga motarsa suka kuma tafi da shi a cikin motarsu.”
Shi ma wani ɗan kwamitin kasuwar, Alhaji Abubakar Garba Karaye, ya ce: “Bayan mun idar da sallar Magriba a babban masallacin kasuwa, sai muka ji ƙarar harbe-harbe.
“Lokacin da muka leƙa, sai muka ga wasu mutane suna harbi a kusa da motar Shugaban Kasuwa.
“Bayan sun gama, suka ɗauke shi suka tafi da shi a cikin motarsu, sun bar tasa motar a kasuwa da harbin bindiga a jikinta.”
Shugabannin kasuwar sun ce ba a taɓa samun irin wannan hari tun bayan kafuwar kasuwar shekaru huɗu da suka gabata ba.
Sai dai kafin wanzuwar kasuwar, an yi ta samun rahoton wasu mutane da ake zargi suna ɓoyewa a cikin dazukan da ke kewayen kasuwar.
Har yanzu ba a samu jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ba, domin ba ya ɗaukar waya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Alhaji Usman Yako Kasuwar Akinyele Kasuwar Kayan Miya Shugaban Kasuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau
Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau.
Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja.
Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar harajiWakilinmu ya ruwaito cewa a yanzu ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada ne zai gaje shi a wannan kujera
ta hakimanci.
Farfesa Ango Abdullahi yana ɗaya daga cikin mazan jiya da suka yi ragowa a Nijeriya.
Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ɗaya ne daga cikin dattawan da al’umma suke buƙata musamman a wannan zamani.
Yana ɗaya daga cikin masu bayyana ra’ayin su a kowanne irin yanayi don jawo hankalin shugabanni da al’ummomi da nufin kyautata rayuwa.
Kazalika, Farfesa Ango Abdullahi shi ne na biyar a tarihin cikin jerin waɗanda suka riƙe muƙamin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Tuni dai Masarautar Zazzau ta bayyana Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada wadda ƙani ne ga shi Farfesa Dahiru Ango Abdullahi a matsayin sabon Magajin Rafin Zazzau.
Sai dai masarautar ta ce zuwa nan gaba kaɗan za ta fidda ranar da za a yi bikin naɗin sabon Magajin Rafin Zazzau.